keffi:- Yadda Rijiya Ta Ci Ran Wata Budurwa A Keffi
![keffi:- Yadda Rijiya Ta Ci Ran Wata Budurwa A Keffi](/blog_images/39454051_1958284600914593_3414077565244014592_n.jpg)
rijiya taci ran wata budurwa a garin keffi
Daga Bashir Isah
Jiya Asabar da yamma marigayiyar (an sakaya sunanta) ta je dibar ruwa a wannan rijiya da ke cikin gidansu inda a nan karen kwana ya cim mata.
Kamar yadda bayanai suka tabbatar, marigayiyar ta hau bakin rijiyar ne tana dibar ruwa wanda a karshe ajali ya fisge ta cikin rijiyar, kuma da kai ta tsunduma ciki wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.
An yi fama matuka kafin a samu halin ciro ta, inda aka yi amfani da tsani fiye da guda kafin daga bisani aka samu nasar ciro ta amma a mace.
Kasancewar da kai ta zurma a rijiyar, an gano ta ji rauni sosai a fuska da kuma wuya. Hakika, faruwar wannan al'amari ya kidima jama'ar Yalwa da ke kusa da GSS keffi, don kuwa har suma mahaifiyar yarinyar ta yi kamar dai yadda wani ganau ya shaida.
A kiyasce dai marigayiyar ta haura shekara 15 da haihuwa. Kuma sai da safiyar yau Lahadi aka yi mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Da fatan Allah ya sada ran marigayiyar da rahama, kana ya kara wa iyayenta dangana da wannan rashi.
Ameen
Created at
![Share Button](http://static.hupso.com/share/buttons/share-medium.png)
This post has no comments - be the first one!