Snack's 1967
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI, SIYASA

labarai:- Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP

labarai:- Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP
- Bangar siyasa ta yi sandin mutuwar magoya bayan 'yan siyasa - Hargitsi ya barke ne yayin da aka so kaiwa kantoman karamar hukumar Brass ta jihar Anambra A kalla mutane uku ne suka mutu a wani karon-batta da magoya bayan jam'iyyar APC dana PDP suka yi jiya a karamar hukumar Brass dake jihar Anambra. Amma sai jami'an 'yan sanda na jihar sun bayyana rasuwar mutum daya ne kawai a rahotansu. Mutane 3 sun sheka lahira yayin karon-batta tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP Sai dai magoya bayan jam'iyyar PDP sun ce mutune uku ne suka rasu sakamakon harin da aka so akai kan mai rikon kwaryar karamar hukumar Brass Victor Isaiah ne.

Sai dai magoya bayan jam'iyyar APC sun ce an kawo wasu mutane ne wanda ba yan asalin karamar hukumar ba, don su tada zaune tsaye. Wanda daga bisani suka far musu da Adduna da kuma bingidu. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Asinim Butswat ya ce "An samu barkewar fada tsakanin wasu matasa da suka ce su magoya bayan APC da PDP ne". "Mutum daya ya rasu, sai guda biyu da suka ji rauni. Kuma ya zuwa yanzu an kai jami'an tsaro yankin domin tabbatar da tsaro". Kakakin 'yan sandan ya shaida.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this