XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 14

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 14
Tarar Aradu Littafi na daya 1 Umar lawan Abdul Typing Shuraih Usman Page 14 . . Toh jama'a sakamakon rashin sauran fallayen littafin hakan yasa, dole da kaina zan karasa maku wannan labari sai ayi hakuri da kura kuran da za'ai arangama da su . Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk daya muke , Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago, Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga cikin gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah idan zamuje sallah nida yayana . Wata rana da asubah na fita sallar asubah nida yayana toh dama ni idan na fita salla nida yayana bama dawowa gida sai safiya domin kuwa tsayawa muke a masallacin muita karatu har sai gari ya waye, kaman kullum yau hakan ta faru, Mun fito muka nufi gida ina zuwa kofan gidan gabana ya buga sakamakon ganin kfan dakina danayi a bude,alhalin kafin na tafi masallaci sai dana sanya dan makulli na kulle dakin gaba daya . Na dai daure na doshi dakin ina bude dakin na saki wani salati sakamakon abunda nagani acikin dakin, Wata mata daga ita sai shimi iya cibiya da wani dingilallen wando iya cinya tana kwance kan katifar barcina, Ina bude dakin matar ta tashi tayi mika, sannan tadan mummustsuka idanuwanta ta dubeni tace yauwa malam kai nake jira dama tun dazu nake son na tafi, . Na dubeta baki bude cikin mamaki nace mata wacece ke sannan meya kawoki cikin dakina, Tayi tsaki tace kaji rainin hankali kadauko ni kuma kana tambayata ko waye ni lallaima, malam ka bani kudina yanzu ina son zan tafi . Ke dan ubanki wani kudin zan baki, yi maza ki fice daga cikin daki yar iskan karya, na fada cikin fusata, Ai nan matannan tai tsalle ta cakumemin gaban riga muka fito daga waje tana cewa wallahi sai ka biyani kudin kwana na, tayaya za'a yi ka dauko ni ka kwana dani sannan kace baza kaa biya ba ai wallahi sai ka biya, . Ba'a bata wani lokaci ba har matannan ta tara min jama'a nan raina ya baci na tsinka mata mari ai ba shiri ta sakeni, na cigaba da jibgarta da kyar mutanen angwa suka kwaceta a hannuna amma duk da haka matannan sai ihu take ita sai na biyata kudinta, a haka yayana yazo ya samemu . Yayi bakinciki sosai kuka ne kawai baiyi ba ya tambayeta nawane kudin bakunya bare tsoron Allah matannan tace dari uku ne, cikin kunan rai yayana ya ciro kudin ya bata, matar ta wuce dakina ta kwashe kayanta tazo wucewa ta dubeni tace Assha, ai wallahi daga yau baka dauko ni dakinka, sai de mu ringayi acan yadda muka saba,tunda kai kace tsiyane aranka,, ko kallonta banyiba donni abun har mamamki nake ni daban taba ganinta ba, . Na dafa yayana nace wallahi yaya....ya katseni ta hanyar daga mani hannu yace umar da na zata abun naka zai tsaya kan sace sace ne toh tunda takai ga sai ka bata bin suna ka kawo karuwa cikin gidana toh ka kwashe naka ya naka ka kara gaba kasan inda dare ya maka daga yau kabar gidannan kenan . Iya tashin hankali yau na gani, kuka ne kawai banyi ba, Cikin kankanin lokaci na shiga shagona na dauki wata tsohuwar jakar kayana, na dauki hanya wacce bansan ina na nufa ba Tafiya kawai nake zuciyata sai radadi take yimin A lokacin da hotunan abubuwan da suka faru dani suke yawo a kwalkwata tamkar a majigi, Duk da ya kasance wunin ranan bansa ka komai a cikina ba, amma hakan bai sa naji yunwa ba Na isa wata angwa na samu gindin wani waje na zauna na kifa kaina a cikin guiwowina, ayayin da tunani iri iri keta zarya a kwakkwana, ji nake tamkar na kashe kaina na huta . ****** Na tashi na nufi wani masallaci domin yin sallar Isha'I domin kuwa yanzu na tabbata mutane ko sun gani ba zasu shaidani ba, bayan na gama sallar ne sai kwanta a masallacin da nufin na kwana a masallacin in yaso gobe da safe sai in wuce kauyenmu wajen iyayena, Mutane daddaiku ne sukayi saura a cikin masallacin har barci ya fara dibana sai naji ana tashi na na dago da kai domin naga waye wannan "Malam tashi koh zamu rufe masallacin ne " Su biyune suna sanye da manyan kaya Kallo daya nai masu na ayyana araina kodai limaman masallacin ko kuma wasu malamai na daban na tashi cikin rashin jindadi na fita daga masallacin na samu wani dan kewaye a jikin masallacin na kwanta, Bayan sun kulle masallacin ne zasu tafi sai naji dayan yace "malam ladan kaga wannan yaro ya koma can ya kwanta kuma, da alama matafiyine don ga shi dauke da Jaka" Wanda aka kira da ladan yace"malam liman kenan ai wannan yaro daka ke gani kasurgumin barawo ne, sau uku ana kamashi a kasuwar kwari, yanzuma daka ganshi anan inaga koh ya lababo ne ya sace mana mita,ko kuma mic" Liman najin haka sai ya rike baki yace "assha " Sai ya daga murya da alama wasu yakewa magana yace "kai samari kuzo ku jibgi wannan mara kunyar barawon, tun kafin ya kassaramu" . Ina jin haka ban san lokacin dana zabura a guje ba na tsallake, dan karamin katangar daya katange gewayin dana ke kwance na ranta ana kare, inajin ihu da kururwan mutane suna cewa atare barawone atare haka na ringa cin uban gudu har na fice daga angwar gaba daya, ina shawarar na tsaya kenan sai naji wani Abu mai nauyi ya bugi kaina daga nan kuma sai ji nayi na kife akan wani ruwa ruwa mai wari, daga jin wannan wari na gane warin giyane ko na aman giya, Idanuna dishi dishi suke gani, wani katon mutum nagani ya tsaya akaina yana rike da wata katako 2 by 2, mutumin ya sunkuyo da kansa daidai kunne na yace "Umar dan wasa daga yau wasanka ya kare , dun kuwa yanzu zan aika ka kiyama, dama sakamakon irinku kenan masu taurin kan tsiya" Ya daga wannan katakon sama da nufin ya buga mini aka......... . Masu karatu anan muka kawo karshen littafin TARAR ARADU na daya 1 Kaman yadda kamin mufara wannan littafi na fada maku cewa 1 and 3 kadai nake da su bani da 2, dun haka gobe zan fara post na TARAR ARADU littafi na uku 3 Allah ya kaimu da rai da lafiya $ TARAR ARADU (m) Umar Lawan Abdul Littafi na daya 1 Typing Shuraih Usman . . Domin download na wannan littafi dama wasu sauran littatafan sai ku shiga shafinmu anan kuyi like Like:- www.facebook.com/hausaebooks
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this