Lamborghini Huracán LP 610-4 t
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 13

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 13
TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 13 aranar unguwarmu sai da daddare nashiga........ ********* ************ ******** Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk daya muke , Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago, Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga cikin gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah idan zamuje sallah nida yayana. Shi kansa rashin jituwa mai karfi ta shiga tsakaninmu. Abisa abunda yakira cimasa mutunci. Nayi masa rantsuwa da Allah akan duk abubuwanbani da hannu aciki yaki yarda. Sai yanzu na fuskanci ashe irin wasan da mutuminnan yake nufi kenan. Hakikanin gaskiya wasan nasa bantaba ganin wanda yakaishi muni ba, sai dai duk wannan bana zaton zan bar farida,domin kuwa kaunarta ta rigaya tabi jikina. Yau iatace rana ta farko dana shirya zanje wajenta tun bayan da'aka yimin sharri. Bakomaine yasa na daga kafa illa tsabar bakin cikin dake damuna. Ahalin yanzu kuka awajena babu wuya domin kuwa da zarar na tuna bana control na kaina abinci ma kadan nake ci. Na isa goron dutse da kimanin karfe tara na dare . Badon komai ysa nayi dare hakaba sai don gudun kada wani wanda yake kasuwar kwari yaganni ya tona min asiri. Tuni su farida rufe gida, nasani abune mai wuya ace wai bacci take kasancewarta mai matukar kwazo, na kwankwasa kofa. Bada jimawaba naji takun kafa "Waye" Aka tambaya muryar farida ce "Umar ne" Na bada amsa tuni ta gama shaida muryata nan da nan ta zare sakata takuma bude kofa kawai naga ta fashe da kuka. Nayi mamakin abinda yasa haka , kodai dun na dade banzo bane? Muka dunguma cikin gida kukantane yafoto da hajiya yau maimakon gaisuwa kuramin ido kawai tayi,ta kuma rike baki "Ashe zaka sake dawowa gidanmu umar, na dauka bazaka kara takowa ba" "Me zai hanani zuwa mummy?" Itama sai naga tafara kwalla "Kai kuma umar hanyar da za'abi da kai kenen" Sai nagane ashe labarin abin dayafaru tuni ya iso garesu.banyi mamaki ba domin kuwa goron dutse unguwace data kushi yan kwari da dama. Nida farida muka zarce daki alokacin datake ta faman cin kuka. "Umar nafadamaka muddin kana tare dani bazaka sami kwanciyar hankali ba amma ka ke keshe kasa kaki yarda to yanzu daka gani da idonka ai ka hakura" Tacigaba da kuka "Dakata farida" Nace da ita "Shin wai kin daina kaunatane ko yaya" Ta tsuguna agabana "Umar bazan daina kaunar kaba har abada" Nayi murmushi "To indai hakane farida banga wani abin dazai sani in janye ba,kisani na dora tubalin soyayyarmune akan gini biyu,imma dai nasami cikar burina imma a kirgani a mutum na hudu daya rasa ransa, kisani ahalin yanzu cigaba da kaunarki ya fiyemin sauki,domin kuwa mutuwa afagen dagar neman aurenki yafiyemin mutuwa asakamakon hauhawar jini" Na sunkuyo gareta "Farida izan narasaki bazankai labaraiba" Kuramin ido kawai tayi tana kallona , unkai tsawon minti daya mun zurawa juna idanu, daga bisani fuskarta ta yaye izuwa murmushi. "Oh! Umar Allah yabar mu tare har abada" Na mayar da murmushinta sa'arda bakina yake motsawa a kokari na lalubo kalmar amin . Tamike tsaye akuma loakci guda da tazauna akan hannun kujerata ta dubeni fuska da fuska "Da ka gujeni umar da mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa babu kai ba " Na girgiza kai "Bazan gujekiba farida har abada koda kuwa za'rika yankan naman jikina (Kaji soyayyar gaskiay kenan Its shuraih 99%)
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this