Polaroid
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 12

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 12
TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 12 Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa. Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai......... Naga saukar ibrahim daga mota kafin mu karaso to menene ya fito dashi? Kodai irin abinnane domin yakama mai kin fitowa da wuri. Na durkusa na gaidashi jamilu ne kawai bai iso ba. Ba 'afi minti biyar ba shima ya'iso akafara hada hada "Kuzo inji alhaji" Ibrahim yafada yana raba mana idanu Muka nufi wajensa cikin rashin sanin abin da kiran ya kunsa. "Ku zauna " Yace damu lokacin daya ke nuna mana benci.muka zauna daura da juna "Bawani abune yasa na kirakuba illa wani abu daya afku wanda banji dadin saba.ya nunani nida jamilu jiya ku na aika cikin motata , to amma dana isa gida sai natarar da abin da baiyimin dadi ba, wanda banga amfanin abar min kes ba alhali an dauke agogon. Wand yin hakan babbar rainin hankaline da bazan juraba . Abin dana keso nasani shin jamilu kaine ka zare agogon ka kai kedin kawai ko kuma umar kaine ka dauki agogon. Kuna iya bani amsa anan izan bahaka ba kuwa kuna iya shaida ma yansan da" Uka kalli juna nida jamilu akuma lokaci guda muka fara rantsuwa ,wallahi mu bamu dauka ba. Alhaji yayi murmushi "To shikenan kuzauna anan " Yazare sailula bisa ga dukkan alamu yana ma yansanda wayane. Bada jimawaba sai gasu sun iso su hudu "Gasunan ku tafi dasu gida jensu ku bincikomin agogona " Aka tasamu agaba . Nidai babban abin daya dameni aga nazo da yansanda gida a matsayin ana zargina da sata.to amma badan hakaba to da ina iyayin komai ma Musamman tunda nasan bandauki agogoba. "Ku hau nan" Yansandan sukace damu lokacin da muka iso gindin motarsu. Bayan mun zauna kan bencinne aka fara tambayar inda za'a nufa . "Ana iya zuwa ko'ina ma " Nabada amsa cikin halin yarda da kaina . "Wanene umar" Daya daga cikin yansandan ya tambaya. Na dora yatsana a kirji lokacin da nake nuna kaina "Gidan ku za'anufa" Dansandan yacigaba da fada. "Dama kana da kyasa kyasan sata harbiyu abaya" Nazare idanu sakamakon jin kazafin da bazai yiwu na musa shi ba.aka sanar da direban inda za shi. Bai gushe yana tuki ba saida muka iso kofar gida. Bakom al'amarin ya sanya tulin yara taruwa, cikin kyarma nasa kuba na bude dakin , tare da yansanda muka shiga. Suka shiga laluben kowanne lyngu da kowanne kusurwa. Badon bakin cikin daya ke cina ba da babu abinda zai hanani dariya. Sakamakon dagewar da yansandan sukayi neman agogo. Wanda hakan tamkar leka tundin kulline domin gano rakuminka daya bata. Tuni sun gama birkita ko'ina amma haryanzu ba'a ga agogo ba. "Muje a duba cikin gida" Daya daga yansandan yafada. "Dakata tukunna" Inji wani dayake kokarin daga katifata.kyalkyalin daya bayyana a karkashin katifar shi yasanar dani akwai wata ajiyar da bansan da'ita ba, Ba komai bane illa kyakkyawan agogo yana walkiya, daukewar numfashina yazo daidai da lokacin dawani radadi ya ratsa kuncina. Sakamakon wani bahagon mari da daya daga cikin yansandan ya kwadamin. "Kace bakai kasata ba" Nan danan bakina yafara fadin abin dani kaina nasan baza a yarda da shi ba. "Wallahi yallabai sharri akayimin" "Barawon banza barawon wofi dama tun sa'arda kazo kake yimana sace sace kaboye kudin alhaji, kaci sailula , yau luma gashi ka saci agogo" Jamilu kenan ya hauni da bambami sa'arda muka fito waje! "Barawo! Barawo!! Mai kasata? Agogo ya sunan ka? Umar" Wata kwarya kwaryan waka kenan da yara suka kirkirota bayan da'aka watsani mota akafara tafiya. Aguje sukabi motan suna raira waka , basu rabu da muba saida muka hau titi. Nasha zagi kala kala da kuma mari dabam dabam kafin mu karasa. Ahaka muka iso har kasuwar kwari daya da ga yansandan na cumuimiye da kuquna . Ya kwadamin mari sa'arda yake kokarin dankwafar dani agaban alhaji "Alhaji yaron tsinannen barawone daya kamata a ladabtar dashi" Yamika ma alhaji agogon kafin kace meye tuni mutani sun cika wajen. Kama daga kwastomomi zuwa masu kanti. "Allah wadaranka" "Allah tsinema" "Allah watsa ka" Sune mabambantan lafuzzan dake fita daga bakin mutane. Wadansu har basa samun daman ganina sabida cunkosan mutane. Zazzafan radadi yarinka bin jikina, ba radadine na zafin duka ba 'a'A radadine na mamakin sharrin da'aka yimin da babu daman na musa shi, babban abinda yafi damuna shine sunana daya riga yabaci akasuwa da unguwarmu,toni yanzu da wacce fuskar zan ringa kallon mutane. "Wayyo Allah umar kacuceni kaci mutuncina" Muryar yayanace lokacin daya iso yana kuka, ya nufo kaina da gudu yansanda suka rirrikeshi. "Ku kyaleni na kasheshi tunda bashi da sauran amfani" Da kyar yansanda suka janyeshi baya "To shikenan daga yau umar na sallameka kar ka kara fitowa indai akwai mutumin da bama shiri dashi bai wuce barawo ba" Alhaji kenan loakci na farko dayayi magana tun bayan isowar mu. Ya sallami yansanda, da sunso abarsu su tafi dani alhaji ya hana 'aka barni anan . Har saida jama'a suka watse sannan na. Tashi, aranar unguwarmu sai da daddare nashiga........ AYYA JIKI MAGAYI DAMA DUK WANDA YACE ZAI TARI ARADU DAKA TO LALLAI SHIMA YASAN SAKAMAKON (Maudu'I) Izan da kaine umar zaka cigaba da soyayya da farida ko ko zakayi hankali Waitin for sharhi Zanci gaba Its shuraih 99%
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this