Old school Easter eggs.
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 11

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 11
TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 11 Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi. Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar yadda muka saba ........ Da rana ta raba sai kuma zafi ya kori sanyi, Wannan yasanya kowa cire rigar daya kara . Muka rarrataye. Da alamun yau alhaji agajiye yake ,domin kuwa tunda yazo ya dare kujera yake ta gyangyadi abinsa. Sailularsa kashe alarm din yayi domin kar adameshi. Kawai ya dorata ahannun kujera . Bai farkaba sai bayan la'asar shima sai da muka yo sallah sannan na tasheshi Yayi mika da hamma sannan yafara lalube-lalube ba musan kome yake nema ba sai bayan daya rasa sannan ya dubemu "Wai ina sailulata take?" "Ina kuka sanya min sailulata" Duk muka yi shiru,kawai sai muka fara rantse-rantse kowa yana fadin bai gantaba.alhaji yafara salati "Da batan sailular nan gwara batan kudin da'aka sayeta,manya manyan abokan mu'amalata ta taurai suna tuntubatane ta wannan layin,akwai kuma nombobi da dama wanda a sailular kawai na shigar dasu,ciki kuwa harda wani mutumin danakeso na tuntuba in anjima don Allah duk wanda yasan inda take yafada zan bashi dubu hamsin" Babu wanda yayi magana acikinmu. Ahaka alahaji yafita akaba da cigiyar sailular duk kasuwa.amma shiru kakeji. Duk yanda akayi de wanine ya lababo ya saceta. Bayan alhaji yadawo daga sallah sai ya zauna akan kucjera. Ko magana ma bayayi saboda tsabar takaici yananan zaune har kusan sallar magriba. Dif nepa suka dauke wuta ba'aganin komai agurin sai dai in ka kura ido sosai zaka hango irin kwaronnan "makyallu" Koriyar wuta nata fita daga bindinsa Yayi kememe abinsa ajikin bango. Jamilu ya tabo ibrahim "dubi hikimar Allah" Wai duk wannan haske daga bindin kwaro yake Ya jinjina kai "Kadan kenan daga hikimarsa" Alhaji ma ya waiwaya wajen domin yagane ma idanunsa , Jamilu kuwa yace sai ya daukoshi. Adai dai lokacin haske yagama kantin sakamakon generator da'aka tayar, To amma kwaron ya shige cikin kaya wutar kawai ake gani. Dana kura ido sanaga ashe ma rigata ya shiga. Jamilu ya laluba ,sai naga ya hada. Gami da fadin "kai" Ya kuma ja dabaya "Menene?" Ibrahim ya tambaya "Ba kwaro bace ashe sailulace" "Wace irin sailula" kuma na tambaya fuska a yakune "Sailula nawa kasani" Jamil yafada loakcin dayake dauko rigar, Akazo da ita gabanmu aka sanya hannu aikuwa sailular alhajice, wai ashe kyallin danjar sabis muke hangowa Alhaji yai gauron numafashi ya mika hannu ya karba , nikuwa alokacin nawa numfashi ya dauke (nima nawa ya kusan daukewa da kyar na seta hanaklina ,lol Shuraih 99%) Akwai kallon yaya haka ? Da fuskokin mutanen ke dauke dashi bayan kallona na tsayin lokaci da alahaji yayi sai kawai yakada kai ya fita . ******* ************** ********* Ahalin yanzu duk wani amincin dake tsakanina da jama'a akasuwa yakau . Hakan bakaramin kuntata min yakeba Alhaji dai yadena aikena ko'ina izan kuwa nazauna kusa da mutum ko carbi ya fitar sai ya mayar da abinsa aljihu. Wai gudun kar na faki idonsa na dauke. Duk inda na nufa kuwa kaga ana C.I.D na hatta da randa izan zan sha ruwa sai atsareni da ido wai duk karna faki ido na tura modar aljihu (hahaha sai ni masoyi shuraih 99%) Kai abubuwan takaici dabam-dabam Ahaka na cigaba da zama cikin zullumi da bakin ciki . Izan kaga na saki raina to tabbata muna tare da farida don gudun karta gane halin dana keciki. Inanan rakube a cikin kanti sai gwani alhaji ya shigo . Da ganinsa kaga babban mutum akwai wani mutum biye dashi alhaji ya mike tsaye suka gaisa Sannan ya sami waje ya zauna "Alahi agogonne na kawomaka" Yafada lokacin dayake duban mai gidan mu "Yauwa! Ansamo" Alhajinmu ya tambaya "Kwarai kuwa" inji wacan mutumin Lokacin dayake karbar wani dan akwati daga hannun mutumin da suka zo tare, Da bude akwatin sai ga wani walwali, agogone na danyen gold mai matukar tsari , Alhaji ya jinjina kai "To shikenan sai mun hadu" Mutumin ya mike "To sai na ganka" Suka yi sallama yatafi alhaji yaba ma jamilu akwatin "Ungo wannan kaimin motata, ka bude aljihy(glove compartment) ka sanya min aciki" Ya karba yatafi ba'a jima ba ya maido wa alhaji makullin "Nakai" Aka cigaba da harkoki anahaka har loakcin sallar la'asar yayi , nida Alhaji muka fara tafiya masallaci da muka dawo sai jamilu da ibrahim suka tafi, Ana haka ne akayo wa alhaji waya ya dauka suka fara tattaunawa, Wani mutunne yakeso abashi cikakken addreshin wani kamfani a ingila Alhaji ya dubeni loakcin daya ke mikomin makulli "Don Allah kaduba kan seat din baya akwai wani karamin littafi kadauko minshi kayo sauri" Na karba na tafi aguje ba'adadeba na dawo da littafin .Alhaji yabashi adreshin sannan yabani na mayar , akacigaba da sabga .har lokacin tashi yayi akabani kudin mota kamar yanda aka saba nakama hanyar gida. ********** ********** ********* Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa. Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai......... YAU KUMA WATA KALUBALECE KE KALUBALAN TAN UMAR Don't trouble troubles Till troubles trouble you Shuraih 99% Zan cigaba
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this