The Soda Pop
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 10

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 10
TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 10 ********** ********** ******** Ahankali kwanaki suka cigaba da zukewa irin zukar da takarda ke yiwa ruwan biro. Ahaka nafara kirga makonni Ko kusa bazaka hada samuna na kasuwa dana makaranta ba.$ Bada dadewaba nafara haskaka kantin. Sakamakon iya mu'amala da jama'a da kuma ilimina hatta kantinan makota idan akayi bakon bature ni suke zuwa su kira. Wannan si yasa akafara yimin lakabi da bakin bature. Na shiga ran alhaji matuka sai yafara aikena wurare dabam dabam sai ya zamto kullum da alhaji yafito toni nagama zama . Jeka nan tafi can kai wannan karbo wancan, kai dade sauransu. Amma duk samunnan danake yi dinki daya kawai nayi. Sauran kudadena kuwa nakan kashesune aharakan hada lefena. Wannan yasanya watarana daya daga cikin abokan aikina yake tambayata "Wai kai umar mai kake da kudine?'Ullum kana samu amma ba'agani jikinka" Nayi dariya "Jamil kenan kowanne mutum kasan yanada manufa, abin dayasa kake ganin halka bawai kwalliya kuka fini son yiba. Bukatun kudi danakedasu shiyasa kukaga ina tattalawa" Yarike baki "Kai kuwa wani irin bukatune wayannan dahar sai ka takura kanaka zaka biya? Nagafa ko aure baka dashi" Nakalleshi "To mai aurene kawai yake da manyan bukatu?ka tsaya idan lokaci yayi zaka gni" Dai dai wannan lokaci alhaji yashigo ,wata kyakkaywar sailulace ahannunsa. Ni dai tunda nake bantaba ganin kan waya mai kyawun na Alhaji ba. Wannan yasanya akullum alhaji yana waya nakan bishoi da ido har yagane yanda nake nuna sha'awata da kan wayar wannan yasanya shi yimin karin bayani akan muhimmancin kan wayar. Ya kuma shaidamin naira dubu dari biyu yasiya nayi matukar mamaki da jin haka . Dubu dari biyu ai kudin kyakkyawar motane . Da alhaji yazo ya tsaya akusa damu Sai naji ashe suna tattaunawa ne da wani mutum mai harkar setlit.zance da akeyima zai kawo setlit ne guda biyar. Kuma duk za a sanyasune a sabon gidan da alhaji yake ginawa. Ni alahaji har mamaki yake bani komai nasa sai ya burgeka.to amma mai zaiyi da wannan sabon gidan alhali ko haihuwa bai taba yiba. Hirar tasu takare akan cewa za'a aikomasa da kudin gobe da rana. (Umar harka fara bani tausayi) Shuraih 99% ********** ************* ******** Ina cikin cin abin ci alhaji yakirani sai yamiko min key din motarsa "Je ka kabude but akwai wata jaka kadaukomin" Nakarfa na tafi da gaggawa Ina dauko jakan saina gane kudine aciki babu tantama sai na baiwa alhaji zan tafi ya tsaidani Ada nayi zaton zasukai miliyan daya ashe dubu dari da hamsinne bako maine yajawo hakan ba sai kasancewarsu yan wazobiya Ya dubeni "Kaga kudinnan kakai wa malam abba mai dishi su" Anan IBB malam abba yake amma naira dari biyu akabani kudin mashin. Nafito na tsaya abakin titi shiru babu wani dan acaba mara fasinja . Wannan yasa na yanke shawarar nafara tattakawa akafa har zuwa loakcin da zansamu dan acaba. Nayi tafiya mai dan nisa . Kawai sainaji anyayimeni nayi sama bansan komaeneneba. Saidai na jini acan gefe guda nayi kokarin namike amma ina juwa ta daukeni dole nakoma na zauna . Sai bayan yan dakiku nayi kiliya .saboda haka na lalubi jakata Amma babu ita kuma babu dalilinta . Tashin hankali shin wai meyafaru danine Bandai san takamaiman abinda ya yayimeniba. Kuma gashi babu mutane a eriyar wajan Na duba jikina babu inda naji ko da kwarzane toni yanzu yazan saka kaina zuwa zanyi wajen alhaji ko kuwa karasawa zanyi inda aka aikeni? Duk biyun dai kusan ma'anarsu daya kusan duk inda naje dai bani da abin fada. Wannan yasa na share waje kawai na zauna (da yafimaka umar lolx shuraih 99%) Ina wajen la'asar tayi.nahada kai da gwuiwa na rasa me yake min dadi. Kawai sanaji ana tabani. Dana daga kai sainaga ashe jamil ne. "Lafiya kazo nan kazauna" Na maida kaina batare dana bashi amasa ba "To kazo alhaji yana kira" Da kamar bazani ba sai wata zuciyarta ce jeka. Na bishi muka rankay zuwa kasuwa. Alahaji ya dubeni "Ya akayine umar nayi waya ance baka kai kudinba" Na sunkuyar da kaina kasa cikin rashin sanin abinda yakamata nafada "Ina kudin suke" Sai naji bakina suna fadin "Sun bata" "Kamar yaya sun bata?" Yatambaya cikin mamaki. Ni kaina nasan bakina yayi gidadanci daya bada wannan amsar. Na bayyana masa duk abinda nasani. Ya dade yana kallona daga bisani ya mike tsaye game da faidn "Allah ya kyauta" ******* ************ ******** Nacigaba da zama akasuwa cikin rashin jin dadi dominkuwa ina fuskantar wani irin kallo daga abokan aikina . Alhaji ma kuma ya canza taku . Ahalin yanzu baya aikena nakai kudi ko kuma na karbo ,nasan bakomai bane ya jawo hakan ba illa bacewar jakar kudi. Wannan yasanya akullum takaicin duniya na damuna . To amma yana iya abin sai hakuri . Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi. Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar yadda muka saba ........ WATA AZAL DIN KUMA Keep following Its shuraih 99% Zan ci gaba
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this