Old school Swatch Watches
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 8

littatafan hausa:-TARAR ARADU littafi na daya 1 page 8
TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 8 Fuskata cike da alamun karaya "Don Allah yallabai ka taimakeni" "To wane tai mako kuma zanyi ma? Kai dana fadamak maganar har taje ma'aikatar ilmi. Katashi kawai kabani waje kaine kajawo wakanka" Nayi tsawon minti biyu awajen banko motsa ba. Daga bisani sai na tattara takarduna na dube shi "To shikenan yallabai Allah ya taimaka" Bai amasa maganar tawaba na fito daga ofis din cike da mamakin wannan lamari. $hakika zancene mara tushe ballantana makama. Kuma lallai anzalunceni ayanda aiki yake wuya. Ballantana kuma a wannan lokaci danake kokarin mallakar masoyiyata farida. Hawaye yazubo min daga idona lokacin danake kokarin barin ginin ofis din. Ahaka nanufi wajen babur dina saidai na yanke shawarar na tura shi waje tukuna. Domin tashinsa anan ciki zai iya juyo da hankalin kowa nikuma banaso aga tafiyata. Nafara turawa ahankali "Mallam umar ina zuwa hakane" Tambayar mai gadi lokacin danake kokarin fita" " zanje nagabatar dawani uzurine" "To adawo lafiya" Ya maido amsa naci gaba da turawa , saida nayi nisa da ginin makarantar sannan na tasheshi. Nahau zuciyata na mai matukar tafarfasa saboda wannan al'amari ahaka na karasa gida cikin rashin kuzari. ********* ********** ********** Nan fa aiyuka suka yimin yawa kullum inafama da matsaloli guda biyu Neman aiki da kuma zaman banza. Aduk sanda nake zaune nakan debe kewa da littatafan hausa na(umar lawan) Kamar su LINZAMiN DAN ADAM' BABBAR MADAFA SaURA KiRIS Kai dama wasu masu dama. Kwanaki suka cigaba da karfa karfa. Akalla ko wacce ta maimaita sau takwas. Wato wata biyu kenan. Amma har yanzu banga wata alama dazata bani karfin guiwa akan samun aiki ba. Na ziyarci kanfaninuwa da ma'aikatu amma shiru kake ji Kai kace wani arnen dajine yaje neman aiki da takaradan tsire . Tuni yan kudaden dake hannuna sun tafi karaye. Wannan ya tilasta min canja salo. Idan wajen dazanje ba mummuman nisane dashi ba nakan daba sayyada. Badon kamai ba sai don tsadar man fetur . Wanda kudin rabin galan sun isheni sati uku ina gwaguya. Da lamari yakai yakawo sai nadaina zuwa ko'ina, Daga gida sai gidansu farida. Ahalin yanzu ina gindin babur dina ba ko'ina zani ba sai gidansu farida. Na tashi babur din bayan dana sha fama. Nahau na nufi goron dutse. Bada jimawaba na'isa gidan Tun kafin na sauka farida tafito domin tarata. Muka rankaya cikin gida . Muka gaisa da babarmu wadda ayanzu sai ka rantse ni ta haifa ba farida ba. Muka zarce falon shakatawa na zabi kujera daya na zauna. Farida ta zauna akan hannun kujerar idanuwanta kyar akaina . Kullum nazo haka take taraiyarayata takasa tsaye takasa zaune. Itace ta zauna ahaguna, Ta dawo dama ta tsaya akaina , ta zauna agabana kaidai abubuwa da bam- da bam nikaina nasan farida tana kaunata irin kaunar da bantaba zaton zata yiminba ta dubeni bayan data ajiye min tataccen lemo "Umar dan Allah ina roko agareka" Na kalleta bayan dana zuki ruwan lemon "Inajinki" Taci gaba "Kaje ka kawo sadaki sai adaura mana aure izan ma baka da kudi bari na baka" Na kalleta a firgice "Farida bari ma wannan zance ni da yanzu bana aiki yaya za'ai nayi maganar aure? Dame zan rikeki farida" Tayi dariya "Kaji ka da wani zance to menene amfanin albashina? Albashina ya ishemu Wajan zama kuwa dama basai nafada ba, mummy ta koma sama sai ta barmana nan kasa idan kuma bakason zama da'ita sai nakama mana haya.$ To me kuma yarage? Ballantana kasan mummy ba'irin sauran mata bane. Kaima kagani dakanka " Nagirgiza kai "Duk naji jawabinki amma ban karbi rokonkiba. Ki kuma tuna nayi miki alkawarin akwati biyar kuma bazan saba ba " Ta dakatar dani "Bari wannan zancen umar aicewa kayi idan kana da hali. Kuma baka dashi yanzu kaga ba saba alkawri kayiba" Nayi dariya "Ai halin danake nufi farida shine rai da lafiya , ahalin yanzu ban rasa ko dayaba" Ta daure fuska " Nidai inhar nizakayiwa to banaso, mummy ma kuma bazata karbaba " Nayi dariya "To mummy din taki ce ke kadai" Ta kalleni "Naji batawabace nikadai ba kuma bari ganin kafini gata agunta dakayi magana sai tace haka za'ayi bama ta sauraron zancena, to wallahi akan wannan bazata goyama bayaba. Kawai saita goyi bayanka akan abin dzaka takura? To akan wannan kam gakucan da mummy arana" Na mike tsaye "To zaki gani nasan yadda zanyi na shawo kanta" Itama ta tashi "Barima zato bazata taba yarda ba" ****** ************ ******* Zama yayi zama tuni kudaden hannuna sun gama karewa . Wannan ya tilastamin saida akwalar baburdina. Na turashi inda akeyimin gyara nace asanyamasa ganye. Haka kuwa akayi. To ashe aiki aka samamin bansani ba Saida nashafe wata guda cur harda kwana shida amma kullum naje sai yace ba'azo an tayaba dana lura sai naga nima in naje har nadawo ko kuda ban taba gani ya sauka akai ba . TOFA GA BABUR INA MAI SAYA SAIYA TUNTUBENI @mr:- shuraih 99%
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this