XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: HAUSAEBOOKS

hausaebooks:- TSATSUBA littafi na takwas 8 Abdulaziz sani m gini

hausaebooks:- TSATSUBA littafi na takwas 8 Abdulaziz sani m gini
TSATSUBA 8
Hausa-ebooks
Littafi na takwas 8
Abdul'aziz sani m gini
Made:- Shuraih Usman


Toh har ila yau muna cikin labarin daya daga cikin MAZAN JIYA, wato jarumi HULKAS MAI HULAN LAMSARA Tare da SARKI SHARDAS jarumin duk duniya wanda babu kamansa

•••••••••••••••••••••••••••••••••
Kadan daga ciki
ba komai ne yasa yarima hulkas ya yiwa kansa wannan tambaya ba face ya tsinci kansa ne a cikin wani wuri mai dauke da kayan kawa na gaban kwatance kuma da ya dubi kasansa sai ya ga babu kasa babu shimfida tamkar akan gajimare yake tsaye kuma dayaga kafarsa ya yi tafiya sai yaji kamar akan daben lu'u lu'u yake tafiya shi dai wannan wuri ya kasance babbar fada wadda ta kayatu ainun ga kujeru na zinare ba adadi a kowacce kusurwar na fadar a bangaren gabas a tsakiyar fadar an girke wata kawatacciyar KARAGAR MULKI ta zinare da aka kawatata sai dai babu kowa akan karagar mulkin wani abun da ya kara daure masa kai kuma yayi matukar bashimamaki shine yadda yaga babu wata alamar kofa wacce za a iya fita ko shigowa cikin wannan fada daya tsinci kansa a cikinta kai tsaye yarima hulkas ya tunkari inda babbar karagar mulkin nan take a tsakiyar fadar Al amin Guyson ina biye dashi a baya, yana zuwa daf da karagar mulkin sai ya risina ya sauke guiyoyinsa kasa ya kwashi gaisuwa a gareta tamkar dama ya ga wani akanta yana mai sunkui da kansa kasa cikin yanayi na girmamawa kwatsam sai yaji an bushe da dariya daga kan karagar mulkin A firgice yarima ya dago kansa yayinda Al amin na matsa baya yayi arba da abinda yake yin wannan dariya ba wani bane ya gani face Aljani Arwasul amsabur a cikin siffarsa ta ainihi Aljani Arwasul masabul ya kasance gabjeje kuma katon gaske mai matukar kwarjini da ban tsoro yana da kaho guda biyu akan tsakiyar kansa kunnuwansa biyu ne dogaye ne tamkar na zomo, amma idanunsa da hancinsa tamkar na bil adama suke fuka fukansa manya ne don zai iya lullube gaba dayan jikinsa dasu hannayansa guda hudu ne haka ma kafafunsa, daga cibiyarsa zuwa kirjinsa siffar zaki ce dashi daga cibiyar kuma zuwa kafafunsa siffar dokine dashi Hm Al amin ahmed Misau nake Typing, kaga kenan ya hada karfi biyu na zaki dana doki, tunda yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin halittar data firgitashi ba ainun kamar Aljani Arwasul masadur Duk da cewa siyama ta taba bashi labarin aljanin amma bai kawo a ransa cewa shine wannan ba tunda bata siffanta masa kamanninsa ba cikin kaduwa yarima hulkas ya dubi Aljanin yace yakai wannan halitta wanene kai kuma akan wanne dalili ka daukoni daga can duniyarmu ta mutane ka kawoni wannan duniyar ta daban? Lallai daka san gagarumin aikin dake gabana da baka rabani da iyayena ka kawoni wannan duniya ba koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai aljani Arwasul masadul ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa kuma ya dakawa yarima hulkas Tsawa al amarin da ya kara firgita shi kenan ainun har ma yaji hantar cikinsa ta fara kadawa cikin alamun fishi Aljani Arwasul madadul ya dubi yarima hulkas yace wane irin yaro ne kai haka mara da a da har zaka rinka yiwa manya tambaya ? Kamata yayi ka zuba ido ka ga yadda zamuyi da kai tukunna ka sani cewa mun daukoka ne domin mu taimaka maka bayan munyi maka jarrabawa ta tsawon kwana uku, koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya zube kasa bisa guiwoyinsa cikin alamun tsoro da girmamawa yace kayimin afuwa ya shugabana idan ka rukeni anan har tsawon kwana uku ba karamar asara zanyi ba yanzu dai kaga gobene da safe yar uwata jaruma siyama za tayi wasanta na karshe da SADAUKI DARKUS a GASAR JARUMTAKA lallai ina son naga yadda wannan gumurzu nasu zai kasance Baya ga haka zamuyi wata gagarumar tafiya mai matukar darari nida..... Caraf sai Aljanin ya tari numfashinsa yace na sani cewa kai da mahaifinka sadauki hailur da mahaifiyarka shadila tare dasu sarki hulbasu kuna son ku tafi neman HULAR LAMSARA to ka sani cewa jarrabawar da zanyi maka a cikin wadannan kwanaki uku indai har ka samu nasarar cinye su ina tabbatar maka zaka sami nasara abisa abinda zaku tafi nema ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa kwana uku anan dai dai yake da jini daya na duniyarku kuma ka sani cewa nan kana inda kake kana cikin wata duniya ne daban dake cikin duniyoyin sama amma kuma zan saukar dakai izuwa taku duniyar domin ka fara fuskantar jarrabobinka, kafin yarima hulkas ya budi baki yace wani abu sai kawai yaji jiri ya kwasheshi kuma idanunsa sun lumshe, kawai sai ji yayi ji da ganinsa sun dauke dif ! Nan da nan hankalinsa ya gushe ya kasa gane halin da yake ciki Al amin Ahmed Misau Bayan cikar yan dakiku kadan kuma sai yaji komai ya dawo masa dai dai yana bude idanunsa ya tsinci kansa kwance a kasa bisa ciyawa a cikin wani kungurmin daji

Domin sanin yadda zata kaya sai ku download na littafin anan kasa ta hanyar danna wannan blue din rubutun
  • DOWNLOAD AS PDF EBOOK
  • DOWNLOAD AS DOC EBOOK
  • DOWNLOAD AS TXT EBOOK
  • .

    Kar dai ku manta littafin kala uku ne' akwai PDF,TXT da DOC Sai ku zabi wanda zai na budewa acikin wayoyinku, batare da mishkila ba .

    Daga:- hausaebooks
    @www.keffians.xtgem.com
    @www.shuraih.waphall.com
    @www.fb.com/hausaebooks
    Release date:- lahadi,19/8/2018
    Share Button Back to posts
    This post has no comments - be the first one!

    Loading...
                     Loading...                  

    Rate this