The Soda Pop
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GIRKE GIRKE

girke girke:- Yadda ake madarar waken soya

girke girke:- Yadda ake madarar waken soya
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana lafiya. Waken soya wake ne wanda yake dauke da sinadarai da dama na gina jiki da kuma kara mata lafiya. Za a iya yin wannan madarar soya din a rika bai wa yara kanana domin yana sanya su kiba da koshi da kuma lafiya. Duk da cewa akwai kayan abinci wadanda ake yi wa yara kanana daga wata shida zuwa biyu, waken soya na saurin sanyasu kiba. Kowace uwa tana son ganin danta ya yi bulbul shi ya sa a yau na kawo muku yadda ake yin waken soya din. Manya ma za su iya sha domin kara musu lafiya. Abubuwan da za a bukata · Waken soya · Siga · Flaba · Madara Hadi A jika waken soya kamar yadda ake jika wake idan za ayi alale ko kosai amma wannan waken daban yake saboda haka, ana iya jika shi na tsawon awa daya zuwa biyu. Sannan a sanya shi a turmi sai a kirba shi kadan domin cire bawon da ke jikinsa. Bayan haka sai a rege shi domin gudun tskuwa sannan a wanke waken carak! Sannan a markada shi ya yi laushi sosai. A sami abin tata ta kamu a tace shi sosai, sannan a sami tukunya a zuba madarar soya a ciki, sannan a debo garin madara a kwaba da ruwa sannan a sake zuba wa a cikin tukunyar. Sai a jira ta tafasa. Tana tafasowa za aga tana yin kumfa sai a rika debe kumfan ana zubarwa sannan a sauke a kasa. Sannan a zuba masa siga dai-dai yadda ake so da kuma flaba na irin kamshin da ake so sai a gauraya har sai sigar ta narke kuma flaba ta ji. A wannan lokacin za a iya bai wa kananan yara. Manyan kuma za su iya sanya ta a gidan sanyi kamin a fara sha domin samun ainihin dandano mai gamsarwa.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this