XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KIWON LAFIYA

kiwon lafiya:- Kallon Bidiyon Batsa Na Rage Kaifin Basirar Matasa – Masana Lafiyar Kwakwalwa

kiwon lafiya:- Kallon Bidiyon Batsa Na Rage Kaifin Basirar Matasa – Masana Lafiyar Kwakwalwa
Wani rahoto ya bayyana gargadin da masana kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa suka yi cewa kallon hotuna da bidiyon batsa a Intanet na canza kwayar halittun ƙwaƙwalwar mutane musamman ma yara da suka balaga. Masanan sun faɗi haka ne a wani babban taron duniya da aka kammala a Rome a kan hatsarin batsa da yara ke fuskanta a duniyar Intanet. Wani babban likitan kwakwalwa a Amurka Donald Hilton ya yi gargadi kan mummunan tasirin da bidiyon batsa a intanet ke yi a ƙwaƙwalwar yara. Shugaban Katolika Fafaroma Francis ne ya jagoranci taron na masana sama da 150 a fannin kimiya da ilimi da al’adu da kuma kare hakkin yara kanana da aka kammala a ranar Juma’ar da ya gabata. A wajen taron masana sun yi nazari tare da tattauna illar kallon bidiyon batsa a ƙwaƙwalwar yara inda suka ce halayyar ƙwaƙwalwa na canzawa a yayin da take nazari ko karatu, kuma yakan zama illa idan aka takura ƙwaƙwalwa. An bayyana cewa matasa na shafe lokaci suna kallon bidiyon batsa domin ƙoƙarin gamsar da kansu ta hanyar wasa da al’auransu da hannu a yayin da suke kallon bidiyon na batsa. Taron ya yi kira ga iyaye su farga su lura wajen ɗaukar matakan kula da dabi’un ‘ya’yansu tare da yin kira ga mahukunta su karfafa dokokin kare kananan yara.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this