Teya Salat
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: WASANNI

wasanni:- Zai yi wahala Manchester United ta yi abin kirki a bana - Scholes

wasanni:- Zai yi wahala Manchester United ta yi abin kirki a bana - Scholes
Magoya bayan Manchester United tare da wasu tsaffin ‘yan wasan kungiyar, suna ci gaba da bayyana rashin kwarin giwar da suke da shi, dangane da samun nasarar United din a kakar wasa ta bana. Tsohon dan wasan kungiyar na baya bayan nan da yayi tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki shi ne Paul Scholes, wanda ya ce ba shakka rashin sayen manyan ‘yan wasa sai sa United fuskantar matukar wahala a kokarin ta na lashe kofuna a bana musamman ma na Premier. Ko a makon daya gabata ma dai kocin kungiyar Jose Mourinho ya koka bisa yadda basu samu nasarra sayen manyan ‘yan wasa ba a kasuwar da aka kare ci, baya ga mai tsaron raga Lee Grant, dan tsakiya Fred da kuma Diogo Dalot. A makon da ya gabata, dan wasan gaba na Manchester United Alexis Sanchez ya ce tilas kungiyar tasa ta sayo ‘yan wasa kwatankwacin Arturo Vidal da kungiyar Barcelona ta saya a baya bayan nan, idan har tana son lashe kofuna a kakar wasa ta bana. Sanchez ya bayyana bukatar ce a dai dai lokacin da ake shirin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa, bayan da mai horar da United Jose Mourinho ya bayyana fatan ‘yan wasa biyu daga kungiyoyin Leicester da Bayern Munich, wato Harry Maguire da Jerome Baoteng.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this