Teya Salat
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KIWON LAFIYA

kiwon lafiya:- Gwamnati ta ciyo bashin dala miliyan 150 don kawar da cutar shan inna a Najeriya -Kemi

kiwon lafiya:- Gwamnati ta ciyo bashin dala miliyan 150 don kawar da cutar shan inna a Najeriya -Kemi
Ministan harkokin Kudi Kemi Adeosun ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ciyo bashin dalla miliyan 150 daga bankin duniya domin kawar da cutar shan inna. Kemi ta sanar da haka ne bayan kammala taron kwamitin zartaswa da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shugabanta a makon da ya gabata. A bayanan da ta yi Kemi ta ce gwamnati za ta yi amfani da wannan kudade ne wajen siyo maganin rigakafin da za a yi amfani da shi wa yara. Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamnatin Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya shirinta na ganin cewa ta kawar da cutar shan inna a kasar ta hanyar wadatar da jihohin kasar nan kudade domin kawo karshen cutar. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da hakan a taron da aka yi don samar da mafita kan hakan. Osinbajo ya ce cutar shan inna ta sake bullowa ne bayan kasa Najeriya ta yi shekaru uku ba’a sami sanarwan sake bullowar ta ba. Ya ce hakan ya faru ne saboda aiyukkan kungiyar Boko Haram da ya hana ma’aikatan rigakafin cutar shiga wasu garuruwa a yankin. Ya kuma ce gwamnatin Najeriya za ta wadata jihohin da duk kudaden da suke bukata domin kawar da cutar gaba daya a kasa Najeriya.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this