Snack's 1967
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

Addinin musulunci:- Cikar Ni’imar Allah Ga Masu Niyyar Yin Layyah – Daga Imam Murtadha Gusau

Addinin musulunci:- Cikar Ni’imar Allah Ga Masu Niyyar Yin Layyah – Daga Imam Murtadha Gusau
Bismillahir Rahmanir Rahim Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai. Muna gode masa, muna neman taimakonsa. Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da miyagun ayyukan mu. Lallai wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma wanda ya batar babu mai shiriya a gare shi. Kuma ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad Bawan sa ne kuma Manzon sa ne. Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai babu shakka, idan watan zul-Hijjah ya kama, shigowar sa ko ganin sa ya tabbata, shugabanni da Allah ya dora wa nauyin yin sanarwa suka yi sanarwa, kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to an hana shi ya rage gashi ko ya aske gashi a jikin sa. Haka kuma an hana shi ya rage farce/kumba/akaifa, ko ya rage wani abu daga cikin fatar jikin sa. Amma ba’a hana mata masu niyyar yin ibadar layyah, yin Kitso ko lalle/kunshi ko sanya turare ba, kamar yadda naji wasu suna fada. Kuma ya kamata mu sani, wannan hukuncin ya shafi mai niyyar yin layyar ne kadai, ban da matansa da sauran iyalin gidan sa. Haka nan hukuncin bai shafi wanda aka sanya shi matsayin mai wakiltar layyar wani ba, koda shine zai yanka. Wannan hukuncin ya shafi mai niyyar layyah ne kadai, ya hada namiji da mace duk daya ne, in ban da maganar kitso da lalle. Hujjah akan wannan shine ingantaccen Hadisin uwar Muminai Ummu Salmah (RA) tace: “Lallai Manzon Allah (SAW) yace: Idan aka ga watan Zul-Hijjah kuma dayan ku yayi niyyar yin Layyah, to ya kame daga aske gashin sa da farcen sa.” [Muslim ne ya ruwaito shi] A wata ruwayar yana cewa: “Kada ya rage wani abu daga gashin sa ko fatar sa.” * Fahimta Da Maganganun Malamai Game Da Wannan Hadisi Hakika malamai sun tattauna, kuma sun karawa juna sani game da wannan Hadisin. Ibn Musayyib yana cewa: Da Rabi’atu Ibn Abdurrahman da Imam Ahmad da Imam Is-haq da Dawud da wani bangare na Mabiya shafi’iyyah sun tafi akan cewa: “Haramun ne ga mai niyyar yin layyah idan watan Zul-Hijjah ya kama ya rage gashi ko farce ko wani abu a fatar sa, har sai ya yanka dabbar layyar sa, saboda Hadisin da yazo a zahiri yana hukunta haka…” [Duba Sahihu Fiqhus-Sunnah wa Adillatuhu, mujalladi na 2, shafi na 375] Sannan Imamu Malik da Imamu Shafi’i, mabiya shafi’iyyah, sun tafi akan cewa: “Yin hakan makaruhine, wato ka yanke farce ko ka aske gashi. Hani ne na karhanci da kyamata, ba haramun bane, saboda Hadisin Nana Aisha (RA)…” [Bukhari da Muslim] Sannan Majalisar Koli ta kwamitin Malaman Kasar Saudiyyah wato Al-Lajnatid Da’imah, sun bada fatawa cewa: “An shar’anta wa mai niyyar yin layyah cewa, idan an ga watan Zul-Hijjah kada ya rage wani abu daga jikin fatar sa ko gashin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa. Saboda Hadisin da Malaman Hadisi guda shida suka ruwaito in banda Imamul Bukhari, daga Ummu Salmah (RA), tana cewa lallai Manzon Allah (SAW) yace: “Idan anga jinjirin watan Zul-Hijjah kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to kada ya rage wani abu daga gashin sa ko farcen sa.”
A cikin lafazin da Imam Abi Dawud da Muslim da Nasa’i suka ruwaito yana cewa: “Wanda yake da abin layyar sa idan watan Zul-Hijjah ya kama kada ya rage wani abu daga gashin jikin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa.” [Duba Fatawa Al-Lajnatid Da’imah, mujalladi na 11, shafi na 397-398] Sannan Imam Muhammad Ibn Hazm (rahimahullah) yana cewa: “Wanda yake so yin Layyah idan aka ga sabon watan Zul-Hijjah to wajibi ne a kan sa kada ya rage wani abu na gashin jikin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa. Amma wanda baya da niyyar yin layyah wannan hukunci bai hau kansa ba.” [Duba Al-Muhallah na Ibn Hazm] Sannan Imam Ibn Qudamah (rahimahullah) yana cewa: “Idan tsayuwar watan Zul-Hijjah ya tabbata, to mai niyyar yin Layyah zai kame daga yanke farce da aske gemu idan kuma yayi hakan to sai ya nemi gafarar Allah, babu fansa a kan sa a bisa haduwar Malamai, kuma ya aikata hakan da mantuwa ne ko da gangan.” [Duba littafin Al-Mugni, mujalladi na 9, shafi na 346] Sannan Imamu Shawkani (rahimahullah) yana cewa: “Hikimar da ke cikin hani akan rage gashi ko farce ga mai niyyar yin layyah shine, domin ya sami cikakkiyar ladar sa ta layyah, na samun ‘yantawa gaba daya daga wuta zuwa Aljannah, domin kuma yayi koyi da mai yin aikin Hajji cikin Ihrami, an hana shi wadannan abubuwa a lokacin aikin Hajji har sai ya gama jifar farko. To kai ma a nan gida sai aka sanya kayi hakan don samun ladar ibadah irin ta shi…” [Duba littafin Nailul Autar na Imamu Shawkani, Mujalladi na 5, shafi na 133] * Nasihata Ga Malaman Da Suke Karyata wannan Sunnah Ta Hana Yanke Farce Da Aske Gashi Ga Mai Niyyar Yin Layyah! Ya ku ‘yan uwa! Lallai ina kira da nasiha ga wadannan Malamai da suji tsoron Allah, su daina izgilanci da Hadisan Annabi (SAW) da sunan bin Mazhaba ko bin wani Malami. Su daina yada irin wannan sabani, domin kaucewa rudani da haifar da rarrabuwa a cikin al’ummah. Suji tsoron Allah, su tabbatar da abinda ya tabbata da ingantattun hujjoji, su daina kore duk wani abu da nassi ya tabbatar da shi, kawai don son zuciyar su da kuma neman a sansu, ko don girman kai, da kin karbar gaskiya. Wannan mas’alah ba sabuwar mas’alah bace. Malamai magabata nagartattu, masu ikhlasi da tsoron Allah sun yi bayanin ta. Don haka, a yau wani yazo da rana tsaka ya nemi rusa abinda ya tabbata kuma ya inganta a Hadisin Annabi (SAW) kawai don son zuciyar sa, ko don dakusasshen ra’ayin sa, sam wannan ba zai karbu ba, kuma al’ummah ba zasu taba yarda da shi ba. Allah ya nuna muna gaskiya ya bamu ikon bin ta, ya nuna muna karya ya bamu ikon guje mata, amin. Wassalamu Alaikum, Allah yasa mu dace, kuma Allah ne mafi sani. Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za ku iya tuntubar Imam a: gusaumurtada@ gmail.com ko +2348038289761.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this