K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GIRKE GIRKE

girke girke:- yadda ake pan cake din ayaba

girke girke:- yadda ake pan cake din ayaba
Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’ Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa girki, shi ya sa a kullum nake kara tunatar da mu a kan cewa yana da kyau mace ta kasance mai sarrafa sabon abu a kullum. Koda tuwo ne, yana da kyau a kasance ana canja na’ukan miya domin kara wa abinci armashi da kuma kin fita ran masu ci. A yau na kawo muku yadda ake sarrafa ‘pan cake’ din ayaba. A ci dadi lafiya. Abubuwan da za a bukata · Ayaba · kwai biyu · Madara · Bata · Sukari · Fulawa Hadi A samu na’urar markada kayan miya (blender), sannan a yayyanka ayabar a ciki. Bayan haka, sai a fasa kwai biyu a ciki, sannan a zuba bata (butter) kamar cokali uku zuwa hudu. Daga nan sai a zuba madarar ruwa ko a kwaba da madarar gari da ruwa sannan a zuba. A zuba sukari da garin fulawa kadan, sai a rufe na’urar a markada su, har sai sun yi laushi sannan a sha. A dora tukunya mara kama girki a wuta (nonstick) bayan ta yi zafi, sai a rika debo kullun ayaba ana zuba shi ta irin yanayin da ake so. Idan ya dan nuna, sai a juya dayan gefen domin shi ma ya gasu. Sannan a kwashe. Za a iya cin wannan hadin da zuma ko da miya. Wannan abincin an fi yin sa ne a matsayin abincin karyawa.a
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
Insane