K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GYARAN JIKI

kwalliya:- yadda za'a magance kaushin fata

kwalliya:- yadda za'a magance kaushin fata
Kaushin fata abu ne da ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi. Akwai abubuwan da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai mayuka da dama wadanda ake sayar da su domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsalolin, fata yau a Duniyan Fasaha mun kawo muku hanyoyi tara (9) wanda zakubi wajen magance wannan matsalar suna nan kamar haka.

1.==>A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a barshi na tsawon mintuna biyar zuwa goma kafin a shiga wanka a kullum.

2.==>A kasance ana diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.

3.==>Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki sai a bari na tsawon mintuna goma sha biyar sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada us din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga cikin jiki.

4.==>A kasance ana amfani da man kwa-kwa a fatar jiki. A daura man kwa-kwa a wuta ya danyi dumi sannan a mulke fatar jiki kaf dashi na tsawon mintuna talatin kafin a shiga wanka a kwanta. A kasance yin hakan a kullum.

5.==>Shan madara kofi daya kafin a kwanta bacci a kullum yana taimakawa fata sosai.

6.==>A kasance ana shafa man kadanya a jiki bayan anyi wanka da daddare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gabadaya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.

7.==>A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi.

8.==>Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar dake da gautsi a jiki sannan yana sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matsa ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon mintuna uku sannan a wanke.

9.==>Ayi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a maka duka a jiki yawan amfani da ababe dayawa a fata yana haifar da kuraje a fata.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
Polly po-cket