Teya Salat
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KWALLIYA

kwalliya:- yadda zakiyi kwalliya izan baki da lafiya

kwalliya:- yadda zakiyi kwalliya izan baki da lafiya
Barkanmu da sake saduwa daku a wannan filin namu na kwalliya wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. A yau na kawo muku yadda za kiyi kwalliya idan ba ki da lafiya. Idan nace rashin lafiya ina nufin wadda batayi tsanani ba. Bai kamata a rika barin fuska da jiki da datti ba don kawai ba’a da lafiya. Idan aka tsaftace jiki ana jin sauki kuma hakan zai iya taimakawa wajen sanya sauki a ciwo. Dole ne a kasance masu tsafta a kodayaushe domin taimakawa lafiyar jiki.

==>Fandesho:Idan rashin lafiyar ta sanya kumburin fuska dasu idanu, yana da kyau a kasance tare da fandesho wadda zai dan boye kumburin fuskar. Bayan anyi wanka sai a samo fandesho a shafa a wajajen da suka kumbura. Yin hakan na dan dadawa fuskar haske.

==> kankara:Idan an kasance ana fama da ciwon ido, yana da kyau a samu kankara a sanya a leda sannan a lullube ta da tawul sannan a dora tawul din akan idanuwan da suka kumbura na tsawon mintuna goma. Hakan zai taimakawa idanu wajen sabe kumburin.

==>Ruwa:Ruwa na da mahimmanci a rayuwar dan Adam. Rashin shan isasshen ruwa na sanya gautsin fata karyewar gashin kai da dai makamancinsu. Yana da kyau a kasance ana shan shayi ko ruwa a lokacin da ba a da lafiya da kuma shafa man jiki domin rage gautsin fata.

==>Man baki:Amfani da man baki yana karawa majinyata kyau. Yana da kyau a rika shafa man basilin a labba domin hana bushewa. Ko kuma a samu wata kala da zata karawa labban kyau sai a yawaita shafawa domin sanya kyawun fuska.

==> Kwalli:Kwalli na dadawa idanu haske. Yana da kyau a rika shafasu a wannan lokutan domin sanya idanu haske da kuma bayyanar dasu.

==>Fandesho da nayi bayani a kai ina nufin ba sai an maka ta sosai ba. Za’a iya shafata samasama ma ya isa. Dama domin a boye wajajen da ya kumbura a fuskar ne.’ Idan mutum yaga cewa ba zai iya yin wadannan abubuwan da na lissafo ba, yana da kyau ya zauna a cikin gida yayi jinyar har sai ya warke bakidaya kafin ya fito waje. Dama muna magana ne akan rashin lafiya mara tsanani.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this