Ring ring
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GIRKE GIRKE

girke girke:- Yadda ake Girka kazan indiyawa

girke girke:- Yadda ake Girka kazan indiyawa
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da su a kan abincin kasashe waje.
Abubuwan da za a bukata
man zaitun
albasa
Kori
Madara(nonon da aka tafasa)
Gishiri
Dakakken masoro
Heaby cream (za'a iya samu a manyan shogunan da ake siyar da kayan girke girke
Kaza daya
Tumatir guda daya
Danyen kori

yadda ake hadawa A wanke kaza sannan a silala ta da kayan kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya. Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai sai a ci gaba da juyawa. A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun zaki.Hmnnn! A ci dadi lafiya!
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this