XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KWALLIYA

kwalliya:- yadda zakiyi kwalliya lokacin damina

kwalliya:- yadda zakiyi kwalliya lokacin damina
Mata da dama ba su cika son yin kwalliya a lokacin damina ba. Domin suna tsoro ka da a fara ruwan saman da zai wanke musu wannan kwalliyar, ko kuma ta cabe musu ita. Sau da yawa ana tambaya wai shin wace irin kwalliya ce ta dace a yi a lokacin damina? Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance wadannan matsalolin ta hanyan sauki.

1.==>Akwai wasu irin hodar fandesho masu santsi kamar mai. Irin su ne ya kamata a yi amfani da su a lokacin damina, domin ko da ruwan ya taba fuskar, ba za ta wanke fuskar ba. A nemi irin wannan hodar fandesho din domin samun sauki ga lamarin

2.==>Akwai wata ‘waterproof mascara’ abin nufi a nan s hi ne ruwa ba ya ratsa cikinta. Irin shi ne ya kamata ‘yan mata da manyan mata na amfani da su a wannan lokacin. Idan ba a yi la’akari da samin irin wannan mascara ba to a sani cewa kwalliyar za ta cabe sosai.

3.==>Kada a manta da lema a duk lokacin da za a fita domin ba za a san lokacin da ruwan zai sauko ba.

4.==>A kasance tare da abin rufe kai. Domin yawan sanya ruwa a gashi ba karamin karya gashin yake ba. Don haka sai a samo wani abu da zai rufe kan yadda ruwan ba zai ratsa shi ba.

5.==>Yana da kyau kuma a san irin takalmin da za a sa saboda jikewa daga ruwan sama. Ana son amfani da takalmin roba, wanda ba zai sa a fadi ba, saboda santsin wuri a lokacin ruwan sama.

6.==>A samu kaya na mutunci wadanda za a sanya a wannan lokacin saboda wani lokacin id an aka jike, kuma idan har tufafin wasu matsatsu kaya ne, sai a ga surar mutum kaf ta bayyana a fili. Yana da kyau mace ta san yadda za ta kula da kanta.

Wannan kasida yana zuwa maku ne daga duniyan fasaha
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this