Polly po-cket
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KWALLIYA

kwalliya:- Yadda za a rabu da tabon fuska cikin sauki

kwalliya:- Yadda za a rabu da tabon fuska cikin sauki
Yadda za a rabu da tabon fuska Wadanda wannan matsala ta fi shafa su ne matasa mata da maza. Sai a ga bayan an sha wahala an rabu da kurarrajin fuska, sai tabon ya ki tafiya. Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliyar mutum. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabbai. Da yawan mutane sun gwada na’ukan mai domin rabuwa da wadannan tabbbai na fuska. Wadansu sun yi sa’a wadansu kuma ba su yi ba. A yau na kawo muku yadda za a rabu da wadannan tabbai na fuska. Ina so a san cewa daya za a zaba daga cikin ababen da zan lissafo kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska.

==>A nika itacen sandalwood, sannan a zuba zuma, a cakuda su.Sannan a shafa a fuska ko a inda tabo yake, bayan minti 30, sai a wanke da ruwan dumi. Itacen sandalwood na tayifar da tabo sosai kuma yana taimakawa wajen haskaka fata. Yawan shafa zuma zalla a tabo ma na batar da shi. Amma sai an yi hakuri domin sauki sai a hankali. Za a iya amfani da wannan hadin na tsawon wata 3 kafin samun biyan bukata.

==>kwallon dabino:Wannan hadin na taimakawa wajen batar da tabo musamman wanda aka samu daga kunar wuta ko ruwan zafi. A gasa kwallon dabino a nika sannan a hada da man kwakwa. Sai a shafa hadin a inda ake bukata. Za a iya samun kamar kwallon dabino 10 a wannan hadin.

==>A samu ganyen dogon yaro sai a hada shi da kurkum sannan a shafa a fuska. A jira na tsawon minti 15 sannan a wanke da ruwan dumi.

==>Za a iya samun markadadden dankalin Turawa a shafa a kan tabo. Hakan na hana kurajen sake fitowa.

==>A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabon. Da wari amma tana aiki sosai a kan fatar fuska ga kuma rabuwa da tabon fuska.

==>A hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

==>A samu ‘aking soda a hada da ruwa sai a shafa a fuska kamar na minti 2 zuwa3. Sannan a wanke fuska.

Daga:- duniyar fasaha
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this