K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

android:- BAYANI AKAN YADDA ZAKA GANO INDA WAYARKA ANDRIOD TAKE BAYAN AN SACETA

android:- BAYANI AKAN YADDA ZAKA GANO INDA WAYARKA ANDRIOD TAKE BAYAN AN SACETA
A wani sabon yunƙuri da kamfanin google na ƙasar Amurka suka yi na sake fito da wata sabuwar hanyar magance satar wayar-komai-da-ruwanka (smartphone) me ɗauke da manhajar Android shi ne na kara wani sabon kalmar bincike a shafin su na google mai suna Find My Android. Wannan kalmar ita ce mutum zai yi amfani da ita a lokacin da yake neman wayar sa, ko ta wurin tunanin wani ya da ɗauke ta, ko kuma ta hanyar neman ta domin rashin sanin inda ya saka ta. Kamfanin wanda suka haɗa wannan tsari da tsarin da suke da shi na Android Device Manager ya na baka damar gano wurin da wannan wayar take, kuma har ya baka damar kiran wayar domin jin ƙarar ta idan mutum yana tunanin cewar wayar tana kusa da shi. Wani ƙarin abin jin daɗi shi ne, shi wannan tsari zai buɗe maka taswirar wurin da wayar take (Map) ta amfani dagoogle Map, ya nuna maka daidai inda wayar take a yanzu, ko kuma lokaci na ƙarshe da google ya sami labarin inda wayar take. Abubuwan da mutum yake bukata a wannan tsari shi ne mallakar gmail account, kamar yadda muka yi bayani a cikin muƙalar mu me taken Android – Tambayoyi 7 Da Mai Amfani Da Wayar Android Ya Kamata Ya San Amsarsua wannan muƙalar mun yi cikakken bayani akan muhimmancin mallakar gmail accountga duk wanda yake riƙe da waya ƙirar Android. Idan kana buƙatar sanin yadda ake buɗe gmail accout za ka iya Duba posts din mu na baya zaka samu bayanin yadda ake bude gmail ta wannan hanya Yadda ake bude Imel na Gmail.

YA Find My Android YAKE?


Find My Android ba manhaja ba ce, kamar yadda aka saba a baya cewar manhajojin da suke iya gano waya idan ta ɓace za ka ga manhaja ce. Find My Android tsarin bincike ne da kamfanin google ɗin suka ƙara a cikin surkullen binciken su. Misali idan mutum yana neman abu a intanet zai shiga browserka wai ya buɓe shafin google ya rubuta abin da yake nema, idan sakamako ya fito sai mutum ya zaɓi wanda ya fi dacewa da kai ka buɗe shi. To shima wannan tsarin neman wayar kusan haka yake, idan kana neman wayarka abin da za ka yi sai ka nemi kwamfuta ko waya mai intanet ka buɗe browser sai ka rubuta www.google.com idan shafin ya buɗe sai ka yi sign inda imel ɗinka nagmail. Shafin google a lokacin da rubuta www.google.com Wannan imel da za ka yi amfani da shi ka tabbatar da cewar shi ne wanda kake amfani da shi lokacin da wayar take tare da kai. Da shi kake saukar da manhajoji da suke Google Play Store. Kasan cewar duk abin da kake yi da wannan wayar gidan google suna lura da shi. Idan shafin ya karɓi abubuwan da ka saka na username da password sai ka dawo ramin da aka ajiye domin yin bincike abubuwa a google sai kawai ka rubuta Find My Android. Wannan shi ne kawai abin da za ka rubuta, da zarar ka gama rubutawa sai ka latsa maɓallin google search daga nan google zai fara bincikar inda ya ga wayar ɗazo ko kuma yanzu.

YA GOOGLE YAKE IYA GANO TA?


Kamfanin google suna amfani da abubuwa guda biyu wanda duk wayar-tafi-da-gidanka tana tare da su, Intanet da GPS. Duk wayar da aka ce Smart phone (wayar-tafi-da-gidanka ) ce to za ka samu tana yin browsing wanda shi ne ma dalilin da ya sa mutane suke son amfani da wayar. Global Positioning System (GPS) wata na’ura ce da ake amfani da ita wurin gano wurin da abu yake ta hanyar amfani da ilimin sanin wuri na Longitute da Latitude. Wannan na’ura ma’aikatu da dama suna amfani da shi, musamman masu fitar da filaye, ko taswirar garuruwa, ko masu neman faɗin wuri kamar masu aiki Ƙasa da Sifiyo da dai makamanta su. To kusan dukkan wayoyin-tafi-da- gidanka suna da wannan na’ura ta GPS a cikinsu, wanda shi ne, mutane ke amfani da shi a Google Map wurin yin tafiya don gano wurin da mutum bai sani ba, ko kuma domin fahimtar adireshin da wani wuri yake. Tunda wayoyin wannan lokaci suna amfani da Intanet da GPS sai kamfanin google suke yin amfani da wannan dama su gano wurin da wayar take.

Share Button Back to posts
Comments:
haji warisu on Thu-30-August-08-2018

INA Amfani da gmail Amma narasa yanda Akaya bana samun damar turama email kome yasa


Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
The Soda Pop