Disneyland 1972 Love the old s
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GYARAN JIKI

gyaran jiki:- Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama

gyaran jiki:- Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama
Premium Times ta rawaito cewa hukumar bada shawara akan bunkasa ayyukkan noma na Najeriya NIFAAS ta yi kira ga mutane da su yawaita shan nonon akuya saboda kara lafiyar jiki da yake yi.

Hukumar ta bayyana cewa Nonon Akuya yafi na saniya amfani a jiki.

Amfanin 8 da nonon akuya ke yi a jikin dan Adam sune:

1.==> Nonon akuya na dauke da sinadarin ‘Protein’ da yafi na nonon Saniya. Yana taimaka wa jiki girma yadda ya kamata musammam ga yara masu tasowa.

2.==> Yana dauke da sinadarin ‘Amino Acids’ da ke kara garkuwan jikin mutum.

3.==> Yana dauke da ‘Vitamin A’ da ke kara karfin ido.

4.==> Yana dauke da ‘Potassium’ da ke kare mutum daga kamuwa da cutar shanyewar gefen jiki, kara karfin kashi, kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini da makamantan su.

5.==> Yana dauke da ‘Phosphorous’ wanda ke taimakawa wajen fitar da ababen da jiki ba ya bukata kamar zufa, fitsari da bayan gida.

6.==> Nonon akuya na da saurin nika abinci a cikin mutum.

7.==> Yana dauke da ‘Magnesium’ da ke taimakawa mutane dake fama da rashin barci.

8.==> Yana dauke da sinadarin ‘Manganese’ da ke kara karfin kashi.

Daga mujallan Duniyar Fasaha
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this