gyaran jiki:- shan lemu mai sukari na haifar da cutar rudewa idan mutum ya tsufa
Shan Lemuna Masu Sikari Na Haifar Da Cutar Rudewa A Lokacin Tsufa
Masana sun gano cewa akwai alaka mai karfi tsakanin shan lemunan da ke dauke da sikari da cututtukan da suka shafi kwakwalwa musamman kamar cutar rudewa da cutar mantuwa.
Wadannan cututtukai dai sunfi kama mutane a lokacin tsufa
A baya dama binciken kimiyya ya alakanta shan irin wadannan lemuna da cututtuka kamar su ciwon zuciya, rubewar hakori, shanyewar jiki, kiba da ciwon sikari.
A yan kwanaki da suka shudene aka wallafa rahotan binciken guda biyu da ke alakanta shan lemuna da cututtukan mantuwa da rudewa (Alzheimer’s and Dementia) a kundin ilimin likitanci biyu masu suna ‘Medical Stroke Journal’ da ‘Alzheimer’s and Dementia’ Wadanda suka gudanar da binciken masana ne a jami’ar koyar ilimin likitanci da ke garin Boston a kasar Amurka.
Daga Mujallan Duniyan fasaha
Created at
Back to posts
This post has no comments - be the first one!