XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

Arba'una hadis:- hadisi na ashirin da biyar 25

Arba'una hadis:- hadisi na ashirin da biyar 25
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﺨﺎﻣﺲ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮﻭﻥ: ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺫﺭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﻧﺎﺳﺎ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺫﻫﺐ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺪﺛﻮﺭ ﺑﺎﻟﺄﺟﻮﺭ، ﻳﺼﻠﻮﻥ ﻛﻤﺎ ﻧﺼﻠﻲ، ﻭﻳﺼﻮﻣﻮﻥ ﻛﻤﺎ ﻧﺼﻮﻡ، ﻭﻳﺘﺼﺪﻗﻮﻥ ﺑﻔﻀﻮﻝ ﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ، ﻗﺎﻝ" : ﺃﻭﻟﻴﺲ ﻗﺪ ﺟﻌﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻜﻢ ﻣﺎ ﺗﺼﺪﻗﻮﻥ؟ ﺇﻥ ﺑﻜﻞ ﺗﺴﺒﻴﺤﺔ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻜﺒﻴﺮﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﺤﻤﻴﺪﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻬﻠﻴﻠﺔ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﺃﻣﺮ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻧﻬﻲ ﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻓﻲ ﺑﻀﻊ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺻﺪﻗﺔ، ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻳﺄﺗﻲ ﺃﺣﺪﻧﺎ ﺷﻬﻮﺗﻪ ﻭﻳﻜﻮﻥ ﻟﻪ ﻓﻴﻬﺎ ﺃﺟﺮ؟ ﻗﺎﻝ: »ﺃﺭﺃﻳﺘﻢ ﻟﻮ ﻭﺿﻌﻬﺎ ﻓﻲ ﺣﺮﺍﻡ ﺃﻛﺎﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﺯﺭ؟ ﻓﻜﺬﻟﻚ ﺇﺫﺍ ﻭﺿﻌﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻠﺎﻝ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺃﺟﺮ«، ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ. HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR: An ruwaito daga Abu zarrin Al'gifariy (R.A) yace: Lallai wassu mutane daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w) sun ce da Annabi (s.a.w), ya Manzon Allah! ma’abota dukiya sun tafi da lada suna yin sallah kamar yadda muke yi, suna yin azumi kamar yadda muke yi, kuma suna sadaka da sauran dukiyarsu, Sai Annabi yace: “ Shin Allah bai baku abinda zaku yi sadaka ba! Lallai dukkan wani tasbihi da za ku yi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ne, dukkan hamdala sadaka ne, kuma dukkan wata hailala sadaka ne, dukkan umarni da kyakkyawa sadaka ne, hana mummunan aiki sadaka ne, kuma a gavar kowannenku akwai sadaka, Sai sahababai suka ce: Ya Manzon Allah! yanzu xayanmu zai biya buqatarsa, kuma ya zama yana da lada? Sai ya ce: Ku bani labari, da ace zai sanya gavar tasa a cikin haram; shin zai kasance yana da zunubi ? to haka, idan ya sanya ta a cikin halal zai kasance yana da lada”, Muslim ya ruwaito shi.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this