XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: WASANNI

wasanni:- Gasar kofin duniya Ga yadda senegal ta fita gasar bana duk da cewa ta hada maki da na biyu a rukunin ta

wasanni:- Gasar kofin duniya Ga yadda senegal ta fita gasar bana duk da cewa ta hada maki da na biyu a rukunin ta
Kasar Senegal ta shiga sahun sauran kasashen nahiyar Afrika da suka fita gasar kofin duniya na wannan shekarar ba tare da sun tsallake zuwa zagaye na biyu.

Hakan dai bai taba samuwa ba a tarihin gasar tun bayan na shekarar 1982.

Wasan ta na karshe na rukuni da Kolombiya, Senegal na bukatar yin kunnen doki ko ta samu galaba domin tsallakewa zuwa zagaye na biyu. Sai dai hakan bai faru ba inda a cikin minti 77 na wasa mai tsaron bayan Kolombiya, Yary Mina, ya zura kwallo a ragar mai tsaron gidan Senegal wanda yayi sanadiyar rashin tsallakewar su.

An kafa tarihi a gasar wannan shekarar sakamakon fitar kasar yammacin nahiyar Afrika bayan wasan ta da Kolombiya.

Senegal ta hada maki daya da Japan wanda da ita za'a tantance kasar da zata tsallake zuwa zagaye na biyu. Japan ta samu galaba kan SEnegal na ketara kasancewa kasar Afrika ta fita samun kati a wasannin da ta buga.

Matakin yana daga cikin ka'idoji da hukumar kwallon kafa na duniya ta kafa a gasar.

Mai horas da yan wasan Senegal, Aliou Cisse, yace ya rungumi kaddarar da ya fada a kan su. A cewar sa babu wata mafita dangane da lamarin domin ka'ida ne wanda FIFA ta kafa kuma kowa ya amince dashi.

"Dokar kwallo ne. Bamu yi nasarar tsallakewa ba domin mun fi samun kati fiye da abokan takarar mu amma, ina alfahari da yan wasan mu. Sun nuna bajinta a gasar bana kuma ina ganin mun nuna ma duniya cewa zamu birge jama'a nan gaba" yace.

Rashin nasara kasar ya jawo bakin ciki a zukatan yan afrika masoya kwallo kafa. Da dama sun bayyana bacin ran su kan sakamakon wasan Senegal da yadda dokar FIFA ta fitar da ita. Gasar bana dai shine na farko bayan shekaru 36 da kasar Afrika bata samu nasara na tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this