Polaroid
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

Arba'una hadis:- hadisi na goma sha tara 19

Arba'una hadis:- hadisi na goma sha tara 19
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﺘﺎﺳﻊ ﻋﺸﺮ: ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺱ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﻛﻨﺖ ﺧﻠﻒ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻣﺎ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻳﺎ ﻏﻼﻡ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻠﻤﻚ ﻛﻠﻤﺎﺕ، ﺍﺣﻔﻆ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﻔﻈﻚ، ﺍﺣﻔﻆ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺠﺪﻩ ﺗﺠﺎﻫﻚ، ﺇﺫﺍ ﺳﺄﻟﺖ ﻓﺎﺳﺄﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺇﺫﺍ ﺍﺳﺘﻌﻨﺖ ﻓﺎﺳﺘﻌﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻋﻠﻢ ﺃﻥ ﺍﻷﻣﺔ ﻟﻮ ﺍﺟﺘﻤﻌﺖ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﻨﻔﻌﻮﻙ ﺑﺸﻲﺀ ﻟﻢ ﻳﻨﻔﻌﻮﻙ ﺇﻻ ﺑﺸﻲﺀ ﻗﺪ ﻛﺘﺒﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ، ﻭﻟﻮ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﻀﺮﻭﻙ ﺑﺸﻲﺀ ﻟﻢ ﻳﻀﺮﻭﻙ ﺇﻻ ﺑﺸﻲﺀ ﻗﺪ ﻛﺘﺒﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻚ، ﺭﻓﻌﺖ ﺍﻷﻗﻼﻡ ﻭﺟﻔﺖ ﺍﻟﺼﺤﻒ« . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﻗﺎﻝ ﺣﺪﻳﺚ ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ. ﻭﻓﻲ ﺭﻭﺍﻳﺔ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ: »ﺍﺣﻔﻆ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺠﺪﻩ ﺃﻣﺎﻣﻚ، ﺗﻌﺮﻑ ﺇﻟﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺧﺎﺀ، ﻳﻌﺮﻓﻚ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺪﺓ، ﻭﺍﻋﻠﻢ ﺃﻥ ﻣﺎ ﺃﺧﻄﺄﻙ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻟﻴﺼﻴﺒﻚ، ﻭﻣﺎ ﺃﺻﺎﺑﻚ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻟﻴﺨﻄﺌﻚ، ﻭﺍﻋﻠﻢ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺼﺮ ﻣﻊ ﺍﻟﺼﺒﺮ، ﻭﺃﻥ ﺍﻟﻔﺮﺝ ﻣﻊ ﺍﻟﻜﺮﺏ، ﻭﺃﻥ ﻣﻊ ﺍﻟﻌﺴﺮ ﻳﺴﺮﺍ« . HADISI NA GOMA SHA TARA: An ruwaito daga Abdullahi xan Abas (R.A) yace: Na kasance a bayan Manzon allah (S.A.W) wata rana sai yace da ni, “Ya kai yaro! Zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah, sai ya kiya ye ka; ka kiyaye Allah za ka same shi a gaba gare ka (yana yi maka jagoranci); idan zaka roqa to ka roqi Allah; idan zaka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani, da al’umma za su taru kan su amfane ka da wani abu, ba za su iya amfanar da kai komai ba , sai da abinda Allah ya rubuta maka. Idan kuma da al’umma za su taru kan su cuce ka da wani abu, ba za su cuce ka ba, sai da abinda Allah ya rubuta maka. An xauke alkaluma, takardun kuma sun bushe”. Tirmiziy [2516] ya ruwaito shi, yace hadisi ne mai kyau ingantacce. A wata riwayar kuma wacce ba ta (Imam) tirmiziy ba, “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani. Ka sani duk abinda ya kuskure maka, to bai kasance zai same ka ba. Duk kuma abinda ya same ka bai kasance zai kuskure maka ba. Ka sani, lallai cin nasara yana tare da haquri, yayewar musiba kuma tana tare da baqin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauki”.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this