Disneyland 1972 Love the old s
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: WASANNI

Wasanni:- Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!

Wasanni:- Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!
- Wasan Najeriya yayi armashi! - An tsorata Najeriya zata dawo gida da wuri - Ahmad Musa ne ya ci duk kwallayen

Wasan da aka gama yanzunnan tsakanin Najeriya da Iceland, an tashi ci biyu da nema, inda Ahmed Musa ya zura dukkan kwallayen a raga bayan wasa mai kyau da hadin kai da Super Eagles din suka taka.

An dai dade ba'a ga irin wannan wasa ba a shafin tarihin kwallon Najeriya, watakil tun zuwansu wasan na farko a 1994, wanda marigayi Rashidi Yekini ya jefa kwallon farko.

A wasan kashi na farko dai, kamar Najeriya baza ta taka wani abin kirki ba, sai dai a karo na biyu, kamar an musu allurar kishin kasa, domin sun san in suka dawo gida a haka zasu ji kunyar idon jama'a sosai.

Garuruwa da Unguwanni dai sun dauki sowwa a duk lokutan da yaro maii tashe Ahmed Musa ya zura kwalayen, bayan sun wahal da turawan na Iceland.

A ranar talata Najeriya zata buga da uwar kwallo Argentina.

Share Button Back to posts
Comments:
Rabiu hamisu kila on Sat-23-June-06-2018

Alhmdllh,yan #NIGERIA mun yi matukar farin ciki da wannan wasa,kuma muna fatan mu dauki #WORLD_CUP

Shuraih99 on Sat-23-June-06-2018

Amiin


Loading...
                 Loading...                  

Rate this