pacman, rainbows, and roller s
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: WAYA

Waya:- Shanyewar batir da yadda ake magance ta

Waya:- Shanyewar batir da yadda ake magance ta
Matsalar zukewar batirin waya da sauri, kin yin cajin batirin cikin hanzari da makalewar manhajoji lokacin son yin amfani da su, kadan ne daga matsalolin da suke addabar masu amfani da wayar Android. Amma In Sha Allahu zamu taimaka wurin kawo manyan dalilai da suke kawo wadannan matsalolin da kuma hanyar magance su.

Tsayar da Manhaja

Abu na farko shine sanin wadansu manhajoji ne suke shanye batir da wuri, sannan mene ne amfanin su a lokacin da suke yin aiki. Domin a wani lokaci mutum zai iya kunnan application a wayarsa kuma bai rufe su ba sannan ya sake bude wadansu. To barin app a kunne suna aiki a karkashin kasa, na daga cikin abubuwan da suke zuke batiri da sauri.

Amma domin sanin wadansu manhajoji ne suke yin aiki a karkashin kasa kuma ya yanayin jan batiri da suke yi, mutum na bukatar ya shiga settings>Battery. Wannan zai sa kaga wadansu manhajoji ne suka fi zukar cajin batir da kuma shin wadanda kake son yin amfani da su, su ne ko kuma wanda dole wayar tana da bukatar su domin ta yi aiki ne?

Idan manhajojin wayar ce ke butakarsu to dole ka yi hakuri ka barsu su ci gaba da aikin su, domin hana su aiki zai kawo matsala ga aikin da ita wayar take yi. Amma idan manhajoji ne wadanda suke taimaka maka wurin yin aiki to sai ka danna force stop.

Akwai manhajoji masu dinbin yawa a Play Store wadanda suke taimakawa wurin sanin hakikanin mai yake faruwa da batirin wayar mutum. Mu a nan zamu iya ba da shawarar saukar da GSAM Battery Monitor. Idan ka saukar da wannan manhajar, zai iya daukan kwanaki yana binciken lafiyar batirin wayar da kuma abubuwan da suke zukarsa. Bayan ya kammala zai baka cikakken rahoto dangane da batirin.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this