Old school Easter eggs.
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

Kimiya da fasaha:- Adadin Yara da ake Haihuwa da Cutar Amosanin Jini a Najeriya - Bincike

Kimiya da fasaha:- Adadin Yara da ake Haihuwa da Cutar Amosanin Jini a Najeriya - Bincike
Wani kwararren Likitan jini dake asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Aliyu Babadoko a ranar talatar da ta gabata ya bayyana cewa ana haihuwar yara 150, 000 masu dauke da cutar amosanin jini watau ciwon Sikila cikin kowace shekara a fadin Najeriya.

Babadoko ya bayyana hakan ne yayin gabatar da wata lacca a jami'ar jihar Kaduna yayin tunawa da ranar Cutar Sikila ta Duniya.

Kwararren likitan ya bayyana yadda cutar amosanin jini ta zamto ruwan dare mai game duniya a halin yanzu.

Yake cewa, akwai kimanin mutane Miliyan 20 zuwa 25 masu dauke da cutar amosanin jini a duniya yayin da kimanin Miliyan 12 zuwa 15 sun kasance mazauna yankin Afirka inda ake haihuwar yara 300, 000 dauke da cutar cikin kowace shekara a fadin Duniya.

NAIJ.com ta fahimci cewa, cikin wannan kaso kasar Najeriya na haihuwar yara 150, 000 masu dauke da cutar amosanin jini inda take dauke kaso 2 zuwa 3 cikin 100 na adadin masu cutar a Duniya.

Wani bincike kamar yadda babban Likitan ya bayyana, kasashen Najeriya, India da kuma Jamhuriyyar Congo na bayar da kaso 90 cikin 100 na adadin masu cutar amosanin Jini a fadin Duniya.

Ya kara da cewa, nahiyyar Afirka ta ciri tuta ta mafi adadin masu dauke da cutar amosanin Jini a duniya hakazalika ita nahiyya kan gaba wajen cutar zazzabin cizon sauro.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this