K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GIRKE GIRKE

Makulashen Azumi:- Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su

Makulashen Azumi:- Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su
Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, Insha Allahu yau zamuyi jawabine akan kunun buda baki kala biyar da yadda ake yinsu. Kunu na daya daga cikin abubuwan da aka fisha a lokacin azumi musammam ma a lokacin bude baki, domin bukatar a dumama ciki a kuma warware kayan hanji. A yau muna tafe da kalolin kunu guda 5 kamar haka;

kunun Madara

Kayan hadi

madarar Gari

danya ko busashshiyar citta

fulawa

lemon tsami

dafaffiyar Alkama ko shinkafa

yadda ake sarrafawa

==> Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba masoro da citta a ciki sai ki bari ya tafaso. ==> Idan ya tafasa sai ki kawo dafafiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya sannan ki kawo fulawa ki kwaba ta da ruwa ki na zuba wa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so. ==> Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan, sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki, sannan ki zuba sikari.

kunun gyada

kayan hadi

gyada

shinkafa

fulawa

lemun tsami

sikari

yadda ake sarrafawa

==> Ki jika gyada ta jiku sannan ki wanke ki cire bawon ta. Sai ki nika ki tace ta. ==> Sai ki zuba wannan tataccen ruwan a kan wuta ki zuba danyar shinkafa, amma idan kina sauri za ki iya zuba dafaffiyar shinkafa, ki na juyawa akai-akai saboda ruwan gyadar zai na kumfa yana tasowa. ==> Idan da danyar shinkafa ne sai ki bari har sai shinkafar ta dahu, amma idan da dafaffiyar shinkafa ce sai ki bari har sai kin ji babu gafin gyadar. ==> Ki dama fulawa da ruwa, ki daure kunun da ita. Za ki na zuba fulawar a hankali har sai kin ga kaurin ya yi miki. Sai ki sauke ki matsa lemon tsami idan ya dan huce, sannan ki zuba sikari. Wannan hanya ce daya kawai da ake yin kunun gyada, akwai wasu hanyoyin daban.

kunun mardam

kayan hadi

garin kunu

citta

kanin fari

lemon tsami

nono

yayan cumi

yadda ake sarrafawa

==> Ki samu ruwa ki zuba a cikin tukunya ki saka citta da ‘ya’yan cumin ki dafa har sai sai kin ji sun fara kanshi. ==> A gefe daya kuma sai ki dama garin kunun, ki zuba nono a kai da dama sannan ki dan kara ruwa kadan, sai ki ringa zubawa a cikin ruwan cittar daya tafasa a hankali, ki rage wuta sosai ki barshi ya yi kamar minti hudu akan wuta. ==> Idan ya yi kauri da yawa kina iya kara ruwa dan kadan. ==> Sai ki sauke, idan ya dan huce sai ki saka lemon tsami. Idan kina so ki na iya saka sikari, ko kuma ki bar shi ki sha haka da gardinsa. Cumin ana samunsa a wajen masu sayar da kayan kanshi a kasuwa ko kuma a kantinan sayar da kayan masarufi.

kunun alkama

kayan hadi

garin alkama da yayan alkama

citta

kirfa

lemon tsami

kanin fari

yadda ake sarrafawa

==> Ki dafa alkama har sai ta yi laushi sosai. ==> A gefe guda kuma ki dora ruwa a wuta ki saka kanunfari da kirfa a ciki. ==> Sai ki samu garin alkama ki kwaba shi da wani ruwan daban. ==> Ki juye wannan alkamar da kika dafa a cikin ruwan kanunfarin da ke kan wuta, sannan ki fara zuba kwabin alkamar ita ma a cikin ruwan a hankali. ==> Ki bar shi ya yi kamar minti uku zuwa hudu akan wuta sannan ki sauke. ==> Idan ya huce sai ki zuba lemon tsami da sikari.

kunun tsamiya

kayan hadi

kayan kunu

tsamiya

sikari

kayan kanshi

yadda ake sarrafawa
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
XtGem Forum catalog