80s toys - Atari. I still have
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GYARAN JIKI

gyaran jiki:- Kula da tafin kafa

gyaran jiki:- Kula da tafin kafa
Kowa na da lokaci irin nasa yanayin fata. Don haka a lokacin da wasu za su yi kaujen tafin kafa daban yake da yadda wasu za su yi na su. Wani a lokacin sanyi yake samun wannan matsalar wani kuma sai zafi ya shigo yake samun kauje. Don haka dole ne a kula da taffuka kafa. Idan ba’a kula tafin kafa yadda ta dace ba kafar za ta fara tsagewa ko kuma fashewa. Mata da dama na mantawa wajen kulawa da kafa a duk sadda suke kwalliya. Me aka yi idan ko’ina ya yi kyau, amma in aka taka mutum sai a ji kafar da kauje ko kuma faso. Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kulawa da tafukan kafarmu kamar haka;

==> Za a iya amfani da ‘baking soda’ (ana samunsa a inda ake sayar da kayan hada ket) da man ‘tea tree’ da man lafinta, sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su, sai a tsoma kafa na mintuna ashirin, sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kauje da faso a tafin kafa.

==> Man lafinta da ‘sea salt’ da ruwan ‘aloe bera’ da man ‘rosemary’ a hada su a ruwa, sannan a tsoma kafa na tsawon mintuna ashirin, sai a dirza kafa har sai kafa ta fita tsaf. ==> Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da tawul. Sannan a shafa man ‘glycerin’ da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa. Sai a yanke farce a gyarasu. ==> A samu man ‘glycerin’ da gishirin ‘Epdomr’ (ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man ‘tee tree’ da kuma man ‘peppermint’ a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin, sai a dauko dutsen goge kafa a dirdirza. Za a ga canji. ==> Shafa man kadanya a bayan an wanke kafa da ruwan dumi, sannan a sanya safa ana kwana da shi. Yin hakan na taimaka wa tafin kafa sosai. ==> A kasance a kullum ana goge kafar da dutsen goge kafa, domin samun tafin kafa mai sulbi da laushi.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this