Snack's 1967
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

FACEBOOK YADDA ZAKA HANA POST NA HOTUNAN BATSA A TIMELINE DINKA

FACEBOOK YADDA ZAKA HANA POST NA HOTUNAN BATSA A TIMELINE DINKA
Hakika, akwai mutane da dama da ba sa son a rika saka sunan su (tag) cikin hotunan da ba su da alaka da su a shafin facebook.

Kasancewar wani lokacin za ka ga wasu daga cikin abokan ka na facebook kan saka hoton da wata kila kai a ganin ka ba shi da wata ma’ana ko amfani kuma sai su yi tag din ka cikin hoton, ko da kuwa kai ba ka so. Kuma kaman yadda muka sani, duk hoton da aka yi tag din ka a ciki, zai bayyana a ‘profile’ din ka ne kai tsaye, wanda hakan ke nufin abokan ka na facebook din za su iya gani, ko da kuwa kai ba ka ‘online’ ko kuma ka dade ba ka bude facebook din ba. Hakan ne ya sa tuni shafin na facebook ya tanadar da hanya mafi sauki da za ka rika dakatar da duk wani hoton da aka yi tag din ka daga bayyana a ‘profile’ din ka idan ba ka so.

Kasancewar babu hanyar hana yin tag din gaba daya. Ga yadda ake yi Yi Login (budo) shafin ka na facebook (a wayar hannu), sai ka nemi wajen da aka sa Settings & Privac yana kasan shafin. Ko kuma kai tsaye ka bi wannan adireshin ta ‘ browser’ din ka � Setting & Privacy A shafin na ‘Settings’, za ka ga inda aka sa Timeline and Tagging, sai ka latsa shi. Bayan ya bude, za ka ga ‘Review posts that friends tag you in before they appear on your Timeline?’..

Za ka ga ‘on’ da kuma ‘off’, sai ka latsa On. Shikenan! Daga yanzu duk lokacin da abokan ka su ka yi tag din ka cikin wani hoto a facebook, to ba zai bayyana a ‘Profile’ din ka ba.

Sai dai za ka ga sanarwa a ‘Notifications’ din ka cewa wane ya yi tag din ka cikin wani hoto. Idan kana son hoton ya bayyana a ‘profile’ din ka, sai ka zabi ‘Add to timeline’. Idan kuma ba ka so sai ka zabi ‘Hide’.

Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this