80s toys - Atari. I still have
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

MAZINACI YA HALAKA IN BAI TUBABA

MAZINACI YA HALAKA IN BAI TUBABA
Mazinaci Da Mazinaciya Idan Ba Su Tuba Ba, Za Su Hadu Da Bala'o'i Guda 15 Kamar Haka :

BALA'O'I GUDA BIYAR TUN DAGA NAN DUNIYA

1Zubewar Imani (hadisi yace duk mai yin zina bashi da imani alokacin da yake aikatawa).

2 Zubewar Mutuncinsu (su kansu sun san cewa basu acikin lissafin mutanen kirki awajen Allah da bayin Allah).

3 . Lalacewar Zuriyyarsu (Duk wanda yayi zina sai anyi da 'Yarsa ko 'Yar Uwarsa ko Qanwarsa).

4. MUMMUNAN TALAUCI : Zina tana haifar musu da mugun talauci. da kuma rashin albarkar duk abinda ya shigo hannunsu

5. MUMMUNAR JINYA : Jinya a cikin zuciyar su (bushewar zuciya), ko kuma a jikin su (kanjamau, ciwon sanyi da sauransu).

BALA'O'I GUDA BIYAR A CIKIN KABARINSU:

1. Rashin Kyawun karko, ko kuma rashin cikawa da Imani (idan ba su yi sa'a sun tuba ba)

2. Tsananin matsi da duhun kabari. (saboda rashin kulawarsu da ibada tun a duniya)

3. Rashin samun kyakyawar addu'a daga bayin Allah. (Allah ba zai sanya tausayinsu a zukatan al'umma ba, balle su tunasu, su yi musu addu'a).

4. Za a nuna musu mummunan mazauninsu a cikin Jahannama tare da sauran Mazinata.

5. Ci gaba da samun karuwar zunubai a kan su saboda alhakin 'ya'yan mutane wadanda suka yi lalata da su suka gurbata musu rayuwa.

BALA'O'I GUDA BIYAR A RANAR ALKIYAMAH:

1. Za a tashe su a cikin kungiyar manyan Mazinata, a karkashin tutarsu. (SUBHANALLAH).

22. Mummunar ruwa mai mugun doyi zai rika fita daga cikin al'aurorinsu.

3. Mummunan Hisabi da wulakantuwa a gaban dukkan halittun Allah, Mala'iku za su yi shelar cewa KUN GA WANNAN MAZINACI NE!! (KO KUMA KUN GA WANNAN MAZINACIYA CE!! ).

4. Za a sanya su a cikin kwazazzabon Jahannama, kuma kunamai da macizai za su rika cizonsu. Ga kuma tsananin bugu daga Mala'ikun azaba.

5. Allah ba zai dubesu da rahamarsa ba..

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Mai nasiha ya rairayo wannan ne daga ingantattun hadisai a cikin Littafin AHWALUL QUBOOR na Ibnul Jawzee da kuma KITABUL KABA'IR na Zahabiy.

Wannan tunatarwa ce. Duk wanda ya ga dama ya dauki hanyar tuba zuwa ga Ubangijinsa. Allah mai gafara ne, kuma mai karbar tuba ne. Dan uwanku a kullum Ahmad Muhammad Dahiru (Moddibbokatagum) daga www.jibwis.org

Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this