Pair of Vintage Old School Fru
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

YADDA AKE SALLAR GAWA

YADDA AKE SALLAR GAWA
'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba. Dan haka ya sa muka ga cewa yana da kyau mu ware mana wani lokaci na musamman, Domin fahimtar da mu yadda ake yin sallar Jana'za.

'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya.

Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.

1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul- fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya.

2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.

3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji.

4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne a kanka da sauran al'ummar Musulmi.

DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.

Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).

Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen

Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this