XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: GIRKE-GIRKE

[girke-girke] AMFANIN MIYAR KUKA DA YADDA AKE YINTA

[girke-girke] AMFANIN MIYAR KUKA DA YADDA AKE YINTA
Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka nada matukar amfani ga lafiyar dan Adam, tana dauke da sinadarai da dama wanda suka hada da ‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da saura da dama. Wadannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutar ciki, ciwon koda, ciwon asthma, majinar dake taruwa a kirji da sauransu. Yara da dama basu cika son miyar nan ba sakamakon Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa, Miyar dai nada gwanin dadi idan aka sarrafata da kyau. Abubuwan da za a bukata wajen sarrafa miyar sune: • Kuka • Banddar kifi • Kaza/nama • Citta • Attarugu • Albasa • Magi • Man shanu • Daddawa Man shanu Hadi Da farko Uwar gida za ta wanke Kazarki ko nama yadda ya kamata sannan ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da daddawa sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da magi. Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo garin kuka a rika kadawa kadan- kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba. Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke. A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this