Teya Salat
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KWALLIYA

Yadda zakiyi kyau batare da kinyi kwalliya ba

post by Shuraih 99%
Yadda za ki yi kyau ba tare da yin kwalliya ba... Mace a koda yaushe damuwarta shi ne yadda za ta ganta ta iya kwalliya da ado. Kuma tana son a duk inda ta shiga idanu su bita da kallo domin ta samu tabbacin cewa ta yi kyau ta kuma iya daukar hankali. Ko kun san cewa yawan shafe-shafe na bata kyaun fatar ‘ya mace? Domin yaye irin wadannan matsalolin shi yasa a yau na kawo muku yadda za a yi kyau ba tare da an yi kwalliya ba ko kuma an yi wani shafe- shafe ba. · Hanya ta farko ita ce mace ta kasance mai yawan shan ruwa a koda yaushe. Koda kuwa sanyi ake yi. Domin yawan shan ruwa na wanke maikon da ke haifar da kurarrajen fuska. · Mace ta kasance mai shafa mai a duk lokacin da ta yi wanka koda kadan ne. Ta shafa a fuska da wuya da hannu da kuma kafafunta domin wadannan wuraren ne suke fara nuna alamun tsufa a jikin mace. · A kasance ana wanke fuska da sabulun wanke fuska a kullum safe da yamma. Yin hakan na wanke ragowar kwalliyar da aka yi. · Kada a manta wanke gashin kai da man ‘shampoo’ kamar sau biyu a sati. Zama da gashi mai datti na sanya amosanin ka da yawan kaikayi a duk inda mace ta shiga da kuma wari. · Kada a manta da amfani da man ‘sunscreen’ a kullum domin wannan man na dauke ne da sinadaren da ke kare kunan rana a fuska da kuma kare fuska daga kodewa ko kuma fesowar kuraje. · A kasance ana shan ruwan dumi da lemon tsami a ciki kullum da safe kafin a ci komai. Yin hakan na karawa mace shekin fata da kuma sulbi. · Yin wanka da sabulu; yana fitar da daudar jiki wadanda suka makale kuma suna hana ramukan gumi fitowa. Yin wanka kullum ya zama wajibi a wajen mace.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this